INGAN TACEN MÀGANIN – ALUMMAN KASAR IRAN SUN FARA BAN KWANA DA CUTAR KORONA BAIROS

Wata tsohuwa mai shekara 103 a kasar Iran ta warke bayan ta kamu da sabuwar cutar coronavirus, duk da hujjar da ya nuna cewa tsofaffi sun fi kasancewa cikin hatsarin kamuwa da annobar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An kwantar da matar wacce ba a bayyana sunanta ba a asibitin da ke tsakiyar birnin Semnan kusan tsawon mako guda.

Amma daga bisani aka sallame ta bayan ta warke ta samu lafiya, kamar yadda aka rahoto Shugaban sashin kimiyar likitoci na jami’ar Semnan, Navid Danayi yana fadi a ranar Talata.

Matar ita ce mutum na biyu da ta warke daga cutar cikin tsoffi a Iran.

Dayan mutumin da ya warke shine wani dan shekara 91 daga Kerman, a kudu maso gabashin Iran, kamar yadda majiyar Legit.ng ta rahoto.

Bayan ya yi fama da rashin lafiya na kwanaki uku, sai ya warke a ranar Litinin duk da cewar yana da wasu rashin lafiya da suka hada da hawan jini

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *