CITAR KORONA BAIROS GWAMNATIN NASARAWA TA KIRA TARON GAGGAWA
Daga Zubairu M Lawal
Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wani sashi na masu ruwa da tsaki ranar Asibar a gidan Gwamnati dake garin Lafia.
Gwamnan yace ; sakamakon cutar ta Korona bairos yanzu abubuwa duk suna kara ci baya a fadin Duniya baki daya.
Yace; harkokin saya da sai da wa duk sun tsaya . kamar yadda kasashe suka rufe iyakoki babu batun cini kayya tsakani .
Yace; abin ya shafi tattalin arzikin Duniya harma da kasar mu Nijeriya.
“A taron da muka gabatar a Abuja an tattauna yadda tattalin arziki ya zama koma baya sakamakon wanan cutar. A saboda haka ne na taraku saboda mu tattauna matsalolin nan da yadda zamu kare Jihar mu da alumman jihar mu daga wanan cutar da illolin ta”.
Da yake zantawa da manema labarai kwamishinan kiwon lafiya ta jihar Nasarawa Dakta Ahmad Baba Yahaya yace; ya zama dole mu fadakar da alumma yadda zasu rage haduwa waje daya ko yayin bukukuwa.
Sanan mu wayar wa kungiyoyin motochin sufuri da kai yadda za’a rika kulawa da daukar fasinjoji a tasha ,Dole a bin cika saboda kada a dau ko mai cutar daga wani guri a kawo shi Nasarawa.
Yace; yanzu mutum biyar da suke kwance a Asibitin Gwamnatin tarayya dake Keffi sun samu sauki suna gab da komawa gida bin cika ya nuna basu da cutar Korona bairos. Rashin lafiya ne da ba a fahinta ba tun da farko
Shima Shugaban Majalisar Sarakuna na Jihar Nasarawa Mai shari’a Sidi Bage Muhammad yace; zasu tara hakimai da dakatai da masu unguwanni su sanar dasu . Saboda su shedawa jama’a a daina cin koso waje guda kuma a rika tsaftace hannaye kafin a ci abinchi.
Suma Shugabannin addinai sun yaba da shawarwarin da Gwamnati ta basu suka kuma ce zasu tara mabiya su sanar dasu .
Mahimmancin tsaftace muhali da tsaftace hannaye da daina yin cin koso a guri guda . su ka ce ba wai Gwamnati ta hanna zuwa wajen adu’a bane , adai nisanta taron mutani ne, saboda rigakafi ya fi magani.