CUTAR HIV KIMANIN MUTUM 150,000 KE KARBAN MAGANI KAYUTA A BENUWE
Inji Dakta Morah
Daga Zubairu M Lawal
Dakta Morah yace acutar HIV tsyi samame cikin alumma jihar Benuwe a shekara ta 2018 kimanin mutani dubu dari da casa’in ke karban maganin cutar kanjamau a jihar Benuwe .
Amma yanzu adadin su ya ragu inda ya koma kimanin mutum dubu dari da hamsi ana kyauta ta zaton mutanin da suka daina zuwa amsar magani sun samu sauki sosai.
Dakta Morah yace; jihar Benuwe ta kasance cikin jerin jihohin da suke fama da cuta mai karya Garkuwan jiki wata HIV.
Yace; abin birgewa suna tsayawa da shan magani Ku a babu fargaba ko shakka .
Ya qara da cewa ; Gwamnatin Nijeriya tana bakin kokarinta wajen taimakawa masu cutar kanjamau da magunguna kyauta .
Yace; suna tabbatar da cewa nan da watan satumba na shekarar 2020 kimanin mutani 45,000 zasu samu wada taccen lafiya suna ma iya yin ban kwana da cutar.
Yace; Babban kudduri Gwamnatin Nijeriya shine nan gaba kadan ayi ban kwana da ire-iren wadanan cututuka masu karya garkuna jiki, dama sauransu masu illata rayuwan Dan Adam.
Da yake jawabi a madadin Gwamnan jihar Benuwe Mista Samuel Orton wanda Kwamishinan kiwon lafiya ta jihar Benue Dakta Sunday Ongbabo ya wakilta.
Ya bayyana jin dadinda da yadda masu cutar a jihar suka kwantar da hankalinsu suna shan magani da zai karya karfin cutar .
Yace; masu shan maganin suna da tunani mai kyau saboda cuta bata son mai shan magani domin idan ana shan magani maganin na karya karfin cutar.
Gwamnatin jihar Benuwe tayi godiya ga Hukumar kula da lafiya ta qasa masamman masu kula da cutar HIV.
A nasa jawabin Shugaban kula da yaki da cutar HIV Babban Darakta a ma’aikatan yaki da cutar Kanjamau Dakta Gambo Aliyu yace matukar alumma zasu kula da shan magani to cutar ba zai samu yaduwa cikin alumma ba.
Wanan cibiaya ta yaki da cutar HIV wanda ake kira NACA tana aiki kafada da kafada da Aisibitochi manyan da qanana tana raba magunguna na masu fama da cutar kanjamau.
Kuma wanan maganin kyautane ba da kudi ake saya ba , mutani suna iya zuwa a binchike su saboda rigakafi yafi magani.
Mutum ba zai san yana da cutar ba sai likitochi sun gwadashi idan akwai su sanar dashi ya riqa shan magani idan babu su sanar dashi babu.
Taron da ya gudana a harabar ofishin NACA dake garin makurdi Babban birnin jihar Benuwe.