MATA ZASU IYA TABBATAR DA ZAMAN LAFIYA A DUNIYA -AMINA MUHAMMAD

MATA ZASU IYA TABBATAR DA ZAMAN LAFIYA A DUNIYA -AMINA MUHAMMAD

Daga  Zubairu M Lawal

Hajiya Amina J.Muhammad Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta yi wannan kira ne a wajen taron tabbatar da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya mai taken mahufofin cigaba mai inganci ga rayuwan marasa galihu karo na 75 , wanda ya gudana a harabar cibiyar yada labarai na Majalisar Dinkin Duniya dake birnin tarayyar Nijeriya  Abuja.

Mataimakiyan Sakataren tace; matsalolin dake faruwa a Duniya yanzu na rashin samar da dau wa mamen zaman lafiya, mata suna da rawar da zasu taka domin samun zaman lafiya mai inganci a ko ina.

Tace; duk abinda naminji zai yi yana karkashin mace ce, haka zalika duk abinda yara zasuyi suna samun tarbiyya ne tun daga gida.

Yara suna samun tarbiyan abubuwa masu kyau daga gida a gaban iyaye kuma suna samu marasa kyau a gaban iyaye. Saboda yaro yana tashi a gaban iyayansa da abinda ya koya.

Hakine akan iyaye su rika sanya ido akan ya’yan su.mace itace da gida ita ke kula da tarboyyan yaran gida . Dole uwa ta riqa sanya ido akan yaran ta ta lura da halayen su ,waye yakeyin mai kyau . waye ya keyin mara kyau.

Tun ice yana qarami ake tan kwasashi yaro yana qarami ake koyar dashi abubuwa masu kyau idan yayi mara kyau a haneshi.

Amma sakaci yanzu iyaye basu damuwa da tarbiyan yara suna barin yaro ya aikata abin da yake so wasu sukan girma da munanan dabi’u .

Haka zalika mace ita zata rika kulawa da maigidanta tana bashi shawara na gari , tana tabbatar da sana’ar da ya keyi .idan yana abu mara kyau idan ta ki masa dole ya chanza ai maza suna samo abubuwan saboda mata ne .

Mace na da dadin baki da zata sasanta tsakanin mazaje da basu jituwa da juna ta haka zata tabbatar da zaman lafiya a tsakanin su.

Taron da ya tara daruruwan alumma maza da mata da yara qanana , Hajiya Amina Muhammad tayi kira ga yara dasu zama masu tausayi da jin Kay da taimakon iyaye , da zuwa makaranta domin samu Ilumi mai amfani .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *