DUK ABINDA YA FARU DA SHEAKH ZAKZAKY LAIFIN GWAMNATIN NIJERIYA NE. INJI ALMAJIRAN SA

DUK ABINDA YA FARU DA SHEAKH ZAKZAKY LAIFIN GWAMNATIN NIJERIYA NE. INJI ALMAJIRAN SA

Daga Ahmad Tijjani

‘Yan Uwa Musulmi a Nijeriya  almajiran Sheikh Ibrahim El-zakzaky ta ce duk abin da ya samu shugabanta a gidan yarin Kaduna to za ta zargi gwamnatin tarayya.

Wasu fursunoni da ke babban gidan yarin Kaduna dai sun tayar da yamutsi inda suka bukaci gwamnati ta sake su saboda fargabar kamuwa da Korona bairos.

Rahotanni dai sun ce an yi yamutsin ne bayan wasu fursunoni sun nemi a sake su suna masu ikirarin cewa wasu fursuna biyu sun mutu sakamakon Korona bairos.

Sai dai shugaban gidan yarin Sanusi Mu’azu Dan-Musa, ya shaida wa BBC cewa batun mutuwar fursunonin ba gaskiya ba ne.

A babban gidan yarin na Kaduna ake tsare da shugaban ‘Yan Uwa Musulmi ta Islamic Movement in Nigeria Sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa.

Rahotannin sun ce ‘yan sanda sun rika harbi a iska da kuma rufe hanyoyin shiga gidan yarin domin hana fursunonin tserewa.

To sai dai a wata sanarwar da ta fito ta bakin Malam Ibrahim Musa ya aike wa manema labarai, ta yi kira ga dukkan hukumomin da ke da hannu a daure Sheikh Zakzaky su tabbatar da tsaron lafiyar malamin da matarsa.

“Za mu dora alhakin kan gwamnatin tarayya idan wani abu ya faru a kansu.

Nauyin kare lafiyar dukkan fursunoni a gidan yari, musamman a lokacin annobar COVID-19 da ta addabi duniya, yana kanta, kasan cewar doka ta ce kowa ba shi da laifi har sai kotu ce ta tabbatar da hakan,” in ji Ibrahim Musa.

Amma Sanusi Dan-Musa, ya ce malamin da mai dakinsa ba sa fuskantar wata matsala.

“Bangarensa daban…Yanzu haka daga wurinsa nake baccinsa yake yi,” in ji shugaban gidan yarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *