Yadda Shugaban karamar Hukumar Lafia ya tsaftace fadar Gwamnatin Nasarawa
Daga Zubairu M Lawal
Sakamakon tsaftace babbar birnin Jihar Nasarawa da kuma samar da tsaro domin dakile ayyukan bata gari ya sanya Shugaban karamar Hukumar Lafia Honorabul Aminu Mu’azu mai Fata ya fatattake duk wani karamin garejin mota dake garin Lafia.
Shugaban karamar Hukumar Lafia yace munyi hakane saboda tsaftace babbar birnin Jihar. Da kuma dakile ayyukan bata gari masu dauko motochi suna daukar fasinjoji a hanya suna cutar da rayuwarsu .
Yace; ba zai yuhu ace babbar birnin Jihar Nasarawa ta zama kota ina garejin mota ba wanan ya zama babu tsaron lafiyan alumma.
Yana da mahimmanci a gudanar da daukar fasinjoji cikin garejin mota .saboda zai baiwa mai hawa mota cikaken nutsuwa ba tare da fargaba ba.
Kuma koda kayan shi ya salwanta yasan gurin da zai kawo kuka.
Wannan aikin gyaran da Shugaban karamar Hukumar Lafia yayi ya sanya cikin garin Lafia babbar fadar gwamnatin Jihar Nasarawa ya qara fadada.
Bayan dokar da ya sanya daga ranar juma’a a ranar Littinin duk inda ake gudanar da daukar fasinja da sunan gareji sun tattara nasu yi nasu sun koma babbar gareji .
Wakilinmu ya giwaya cikin garin Lafia a ranar Littinin ya kuma ganewa idanun sa yadda jama’a suka bi ummurni suka shafawa kansu ruwa domin tsira da mutumchi.
Guraren da wakilinmu ya giwaya sun hada da garejin On the move da garejin Akurba wanda take kan hanyar Shandan cikin birnin Lafia.
Sanan tarin gareji da suke kan hanyar jos duk sun tashi , daga saboda tarin garejin a wanan hanyar sun kai goma suna daukar fasinjan Abuja ko Jos.
Wakilinmu ya zanta da wasu mutani da sukace, sunana Alhaji Sabi’u Ahmad gaskiya gyara ne yayi dai dai . saboda masu motochi sun mai da ko ina ya zama garejin mota abin babu tsari.
Ko kofar gidan mutum zakaga an an ajiye motochi ana daukar fasinja.
Shima Victo Devid yace; yanzu duk mai bukatar hawa mota sai yaje gareji saboda zaifi masa kwanciyar hankali.
Itama Maryam Sule, tace ; yanzu muna da tabbaci zamu hau mota hankalin mu kwance babu fargaba.
Muhammad Nasiru yace ; Gwamnati sai ta gyara garejin motar saboda ya zama na zamani. Domin garejin ba zai dauki yawan motochin da suka koma can ba.
Musa Ahmad yace ; Gwamnati ta kyauta da ta samar da tsarin daukar fasinja cikin garejin mota wanan zai kawar da harkan ta’addanci da wasu keyi da qananan motochin su.
Hajiya Lantana ta yabawa Shugaban karamar Hukumar Lafia Honorabul Aminu Mu’azu mai Fata tace ayyukan da ya samo cigaba ne ga alumman Jihar saboda zasu samu dama shiga mota a waje guda masu zuwa zasu sauka a waje guda.