BAN YARDA DA ROHOTON KWAMITIN KAN MACE-MACEN KORONA A KANO BA – GANDUJE

Ban Yarda Da Rahoton Kwamitin Buhari Kan Mace-Macen Kano Ba- Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rahoton gwamnatin tarayyar kasar da ya gano cewa cutar korona ce ta yi ajalin kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen da suka mutu a baya bayan nan.

A wata sanarwa da ya fitar, Abba Anwar, mai magana da yawun Gwamna Ganduje, ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin yin bincike kan mace-mace ya gano cewa kusan kashi kashi goma sha shida cikin dari ne suka mutu sanadin korona.

Gwamnan ya ambato kwamitin yana cewa: “Mutum 255 cikin 1604 da suka mutu, wato kashi 15.9… ne suka mutu sanadin cutar korona. Wasu daga cikin mace-macen suna da alaka da rashin samun magunguna da kuma dakatar da harkokin rayuwa da na kasuwanci saboda fargabar annobar korona.”

KU KARANTA DAKATAR DA ADAM OSHIOMHOLE JAM’IYYAR APC BATA DA MAKOMA A JIHAR EDO DA NIJERIYA.

A makon jiya ne Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano ya nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan sanadin mace-macen da ba a saba gani ba a jihar.

A cewar ministan, an samu rahotonnin mutuwar ne a ƙaramar hukuma takwas na cikin birni a watan Afrilu.

Ya bayyana cewa an riƙa samun mutuwar mutum 43 a kullum lokacin da cutar na kan ƙololuwarta kafin daga bisani adadin ya zama mutum 11 a kowacce rana.

A watan Afrilu Shugaba Muhammadu Buhari ya aika kwamitin na musamman zuwa Kano don gano sanadin yawaitar mace-macen, sannan ya sanya dokar hana fita ko da yake daga bisani Gwamna Ganduje ya kyale mutane su ci gaba da fita a wasu ranaku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *