MASU GARKUWA DA MUTANI SUN KASHE JAMI’IN SHIGA DA FICE A NASARAWA

MASU GARKUWA DA MUTANI SUN KASHE JAMI’IN SHIGA DA FICE A NASARAWA

Daga Zubairu M Lawal

A Daren jiya ne mahara masu Garkuwa da mutani suka kai samame gidan Dan uwan Dan takarar Gwamnan jihar Nasarawa a inuwar Jam’iyyar APGA.

Maharar sun kai samamen ne da misallin karfe 9: na dare a gidan Salisu Usman Maku wanda ya’yane ga Labaran Maku da ke zaune a garin Gudi inda nane mahaifar Gwamnan jihar Nasarawa a qaramar hukumar Akwanga.

Maharar sun kashe yar Salisu Usman Maku nan take sakamon harbi da sukeyi kan mai uwa da wabi.

Daga bisani sukayi garkuwa da yaron sa da kuma matar Dan nasa wanda shi yana aiki ne a Rundunar Jami’in shiga da fice na kasa a jihar Nasarawa.

Bayan tafiya da Usman Salisu Maku tare da matarsa Maharar sun kashe Usman Salisu maku suka kuma cigaba da yin garkuwa da matar tasa.

Wanda har ya zuwa lokacin hada wannan labarain babu labarin cewa an ga matar Usman Maku.

Shugaban Jami’an shiga fice ta jihar Nasarawa Zainab Lawal ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin Jami’an ta da masu Garkuwan suka kashe.

Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da afkuwar lamarin a tabakin Jami’in Hulda da Jama’a Mista Ramhan Nansel

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *