ABIN TAUSAYI – YADDA AMBALIYAN RUWA YA CI GIDAJE SAMA DA 25 A LAFIA JIHAR NASARAWA

YADDA AMBALIYAN RUWA YA CI GIDAJE SAMA DA 25 A LAFIA JIHAR NASARAWA

Daga Zubairu Lawal

Batun yadda ruwan sama ke ambaliya a gidajen mutani a garin Lafia fadar Gwamnatin jihar Nasarawa ba sabon abu bane.

Kusan a duk shekara sai ruwa yayi ambaliya a gidajen al’umma wani lokacin ya tsaya a dunbin asarar dukiya  wani lokacin yakan ci rai.

A ranar Asabar ranar da Gwamnatin jihar Nasarawa ta kebe domin gudanar da dokar tsaftace muhali na karshen wata. An wayi gari da ruwan sama kamar da bakin kwarya. Wannan ruwan da akayi ya ci gidaje sama da 25 a unguwanni dabam dabam.

Wani gidan da ruwa yaci ta kai ga saida aka hada da hukumar kwana-kwana sukazo da mota suna zukar ruwa suna zubarwa a wani gurin.

Wakilinmu ya garzaya gurin inda ya ganewa idanunsa yadda rawan sama ya shanye wannan gidan dake kantitin U.A.C. dake Doma Road.

Wani mazaunin gidan yace da kyar ya iya fita saboda ruwan ya kawo masa iya wuyar sa. Ya ce tun misalin karfe uku da rabi ruwan ya fara zuwa, da “mukaga ruwa ya fara shiga dakunanmu sai muka rika futa zuwa waje lokacin da na haura sama sai babu hanya, cikin taimakon Allah na shiga ruwan ya kawo min har wuya”.

Gidan Xan Bala Ahmad kimanin dakuna uku suka rushe amma babu asarar rayuka.yace” lokacin da ruwan ya yi yawa sai mukaga katangarmu ta rushe muna fita da yara sai dakin yara qanan itama ta rushe Allah yasa duk sun fita. Yanzu har gidan makwafcinmu shima ya rushe shagunan kasuwancin mu duk ruwa ya cika”.

Bayan gidajen mutani ambaliyan ruwan ya mamaye Makabartan kofar Makama sannan ruwan yayi ambaliya a gadar da ta hada hanyar Lafia zuwa Doma.

Ko a bara an samu irin wannan ambaliyan a wannan gadar inda Gwamnan jihar Injiniya Abdullah Sule ya ziyarci gurin ya ga yadda aka samu asarar rayuka da dukiyoyi ya kuma yi alkawarin zai gyara a kara fadi da tsawan gadar amma shuru kakeji.

Ko a makon da ya gudana jaridar Leadership Ayau ta kawo labarin yadda zaizayar qasa ke barazana ga rayukan al’umma a jihar Nasarawa.

Sakamakon akwai karancin hanyoyin ruwa masamman a babbar birnin jihar. Sannan mutani sukan cika hanyar ruwa da shara. Da zarar suga hadarin ruwa sun dinga zuba shara ke nan ko a kan tituna.

Kwamishinan tsaftace muhali ta jihar Nasarawa Honorabul Musa Ibrahim Abubakar ya sha gargadin mutani da umurtansu su dinga gyara kwalbatin saboda ruwa su daina zuba shara amma sukanyi kunnin uwar shegu.

Kwamishinan ya jajantawa mutanin da suka samu asara na ambaliyan ruwa a wannan lokacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *