MAJALISA ZATA BINCIKEN MATAIMAKIN GWAMNAN NASARAWA KAN KUDIN YAKI DA COVID-19
Daga Zubairu M Lawal
A jiya talata Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta kafa kwamitin mutum shida domin binciken yadda Shugaban yaki da annobar cutar Korona bairus da kwamitin sa suka kashe zunzurutun kudi har sama da naira miliyon 500.
Shugaban kwamitin yaki da annobar cutar Korona bairus wanda mataimakin Gwamnan jihar Nasarawa Dakta Emmanuel Agwado Akabe shi ke jan ragamar ta yi rabon goro da kudaden da aka samar domin yaki da cutar a jihar.
A ranar alhamis 25-6-2020 Mataimakin Gwamnan yayi jawabi gaban manema labarai inda ya bayyana hanyoyin da suka raba naira miliyon milyon 536.156 haka.
A fadan sa ya ce an baiwa Ma’aikatan kiwon lafiya ta jihar naira miliyon 253,890,000
Sannan ma’aikatan yada labarai ta jihar ta samu naira miliyon 3,530,000.
Ma’aikatan aikin Gona ta jihar ta samu zunzurutun kudi naira miliyon 134,350.000
Ma’aikatan tsaftar muhali ta samu naira miliyon 21,8000.
Babban Asibitin Dalhatu Arfa dake garin Lafia ta samu naira miliyon 3,530,000.
Cibiyar da aka ware domin kulawa da Korona bairus da yan kwamitin sun tashi da naira miliyon 1,850,000
Ma’aikatan Shari’a ta jihar ta samu naira miliyon 74,981,000
Ofisin Shugaban ma’aikata ta jihar ta samu naira miliyon 3
SDG, ta tashi da naira miliyon 32,2880,000
Haka zalika (ICT) Ta samu naira miliyon 1,270,000
qaramar hukumar Karu ta karbi naira miliyon 4.5
qaramar hukumar Nasarawa ya tashi da naira miliyon 3
Majalisar ta bukaci ayi mata cikaken bayani kan yadda aka kashe wannan kudin ba kqmar yadda aka fada a baki ba. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Honorabul Balarabe Abdullah ya bayyana haka bayan kuddurin da Dan Majalisar mai wakiltar mazaber Kokona Honorabul Daniel Ogazi ya gabatar.
Kakakin Majalisar Alhaji Balarabe Abdullah ya ce wajibi ne Majalisar tayi bincike yadda kwamitin yaki da Korona bairus ta kashe kudin saboda al’umman jihar Nasarawa zasu gamsu da yadda ake yaki da annobar cutar Korona bairus a jihar.
Kwamitin binciken zai gudanar da aikin sane a karkashin Jagorancin Honorabul Abdullah Angibi mai wakiltar mazaber Lafia ta tsakiya.
Mai taimakin shugaban kwamtin binciken Honorabul Usman Labaran Shafa mai wakiltar mazaber Toto/ Gadabuke.
Sai Sakatariyar kwamitin binciken Barr Safiya Balarabe
Sauran Membobin kwamitin sun hada da Honorabul Ibrahim Aga Muluku da Daniel Oga Ogazi da Abdul’aziz Dan Lami.da Honorabul Sulaiman Yakubu.
Kakakin Majalisar Honorabul Balarabe Abdullah yayi kira ga kwamitin da su gudanar da binciken tsakin da Allah domin hakine da ya rataya garesu na cigaban jihar Nasarawa