GWAMNA ABDULLAH SULE YA YI KIRA GA AL’UMMAN JIHAR DA SU KARA HAKURI KAN BATUN TAFIYAR GWAMNATIN SA
Daga Zubairu Lawal
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka ne a lokacin da yake rattaba hannu akan kasafin kudin bana da aka rage ya zuwa naira miliyan dubu sittin da miliyan dubu biyu
Gwamna Abdullah Sule yace rage kasafin kudin ya biyo bayan matsalar tattalin arziki ne da annobar cutar COVID-19 ta jefa kasar nan ciki.
Gwamnan ya ce rage kasafin kudin ya zama wajibi saboda tattalin arziki jihar ya shiga tangal-tangal. Saboda zaman gida da dokar kulle ta sanya duk hanyoyin kudaden shiga sun tagayyara.
Gwamna Abdullah Sule yayi roko ga al’umman jihar Nasarawa dasu kara hakuri saboda yadda tsarin tafiyar Gwamnatin sa baya fatan gudanar da abubuwa cikin gaggawa wanda ba zai kai ga cin nasara ba.
Gara abi komai daki-daki ta yadda kowa zai ji dadi ya amfana da ayyukan cigaba.
Gwamnan ya yabawa yan Majalisar dokoki na jihar Nasarawa masamman Kakakin Majalisar Honorabul Balarabe Abdullah kan yadda suka hanzarta duba batun rage kasafin kudin kuma suka aiwatar cikin gaggawa domin cigaban al’umman jihar.
Shima kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa Honorabul Balarabe Abdullah ya ce ganin mahimmancin wannan kasafin ya sanya suka katse duk wasu ayyuka suka gudanar da batun kasafin.