BURIN MU TABBATAR DA ZAMAN LAFIYA A YAN KIN AREWA MASO GABAS

BURIN MU TABBATAR DA ZAMAN LAFIYA A YAN KIN AREWA MASO GABAS

Mista Kallon

Daga Zubairu M Lawal

Babban kodineta a ofishin Majalisar
Dinkin Duniya mai kula da tsare- tsaren ayyukan ta a Nijeriya Mista Edward Kallon ya tabbatarwa Duniya cewa babban burin sun na Ma’aikata a ofishin Majalisar Dinkin Duniya samar da zaman lafiya yankin Arewa ta gabas.

Mista Edward Kallon ya ce samun zaman lafiya a yan kin Arewa ta gabas zai samar da zaman lafiya a fadin tarayyar Nijeriya dama makwaftar ta.

Ya ce jihohin Adamawa da Borno da Yobe suna bukatar jajir cewa da taimakon al’umma wajen samar da zaman lafiya mai durewa.

Mista Edward Kallon ya ce zasu cigaba da baiwa Gwamnatocin yan kin Arewa ta gabas dukkanin tallafi da shawarwari ta kowani hanyar da zai tabbatar da zaman lafiya wannan yan kin.

Mista Kallon ya bayyana hakane a lokacin da ya ziyarci gidan Gwamnatin jihar Borno a wani tattaunawa.

Ya ce duk wani ayyukan cigaba da Gwamnatocin yan kin Arewa maso gabas sukeyi na cigaban qasa da al’umman jihohin su ba a gani saboda rashin zaman lafiya da ya addabi al’umman yan kin.

Ya qara da cewa rashin zaman lafiya ya sanya al’umman yan kin sun hijira zuwa wasu gurare domin gudanar da rayuwar su cikin sauki.

Mai ba da shawara kan harkokin  tsaro na hukumar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin nahiyar Afirika Mista Trond Jensen wanda ya wakilci Babban kwamnadar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya Mista Robert Marinovic ya yabawa Gwamnatin jihar Borno da na Adamawa da Yobe.

Ya kuma ce zaman lafiya wannan yan kin abune da yake da mahimmanci ga al’umman Nijeriya. Ya kuma yaba da irin tallafin da kungiyoyin sa kai sukeyi da masu fadakarwa wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a wannan nahiyar ta Arewa maso gabas da Afirika.

Hajiya Hadiza Aminu Dorayi ta qara jinjina maganar Mista Edward Kallon na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yan kin Arewa maso gabas.

Ta ce al’umman yan kin Arewa maso gabas da suka hada Adamawa Borno da Yobe mafiya yawansu da suka tsira suna rayuwa ne cikin kunci.

Wasu na rayuwa a sansanin yan gudun Hijira wasu kuma sun bar garuruwan su sunje wasu guraren suna zama.

Tawagar ta yabawa Gwamnan jihar Borno Alhaji Babagana Umar Zulum saboda yadda yake jajircewa domin hadin kan al’umman jihar Borno da tabbatar da zaman lafiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *