Nijeriya tayi nasarar yaki da cutar shan-inna
Daga Zubairu M Lawal
Gwamnatin tarayyar Nijeriya tayi bikin murnar yaki da Annobar cutar Shan-inna Wanda yake addabar yara kanana.
Gwamnatin tarayyar Nijeriya tayi bayyana irin jajircewar da tayi wajen kulawa da bada magunguna da gudanar da aluran Rigakafin cutar Shan-inna a kan lokaci.
Nijeriya tana daya daga cikin qasashen nahiyar Afirika ta yamma da suka samu nasarar kawar da Annobar cutar Shan-inna a Kasashen su.
Cutar Shan-inna da yayi kamari a wasu jihohin Nijeriya da suka hada da Jihar Lagos da jihar Sokoto sun tabbatar da magance matsalar cikin gaggawa.
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta hada giwa da Gwamnatocin jihohin da kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da sauransu masamma hukumar kiwon lafiya ta Duniya ta taka mahimmin rawa wajen ganin anyi nasarar yaki da cutar Shan-inna a Nijeriya.
Cikin shekarar 2020 tarayyar Nijeriya ta dakatar da gudanar da Alurar Rigakafin cutar Shan-inna a fadin kasar sakamakon babu masu cutar, kwata-kwata.
Hukumar kula da kiwon lafiya ta Duniya wato (WHO) ta tabbatar da nasarar yaki da cutar Shan-inna a Nijeriya inda tace yanzu zata fuskanci kasar Madaganka domin kawo karshen cutar a kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa Gwamnatin Nijeriya kan yadda ta rika shiga birane da karkara lungu da sako wajen baiwa yara maganin yaki da cutar Shan-inna.