Muhawarar majalisar Birtaniya kan EndSARS ta ja hankalin ƴan Najeriya
Muhawarar da majalisar Birtaniya ta yi kan rikicin EndSARS ta ja hankalin ƴan Najeriya musamman batutuwan da aka tattauna a zauren majalisar.
Ƴan majalisar sun yi muhawara ne a ranar Litinin kan wata takardar koke da mutum fiye da dubu 220 suka sanya wa hannu da ke neman Birtaniya ta ɗauki mataki kan zargin kashe masu zanga-zangar a Najeriya.
Ƴan majalisar ta Birtaniyar sun amince cewa ya kamata gwamnatin ƙasar ta dubi yiwuwar sanya wa jami’an Najeriya takunkumin karya tattalin arziki waɗanda ke da hannu a buɗe wa masu zanga-zangar EndSARS wuta.
Sai dai wannan mataki na majalisar ba tilas ne gwamnatin Birtaniya ta yi aiki da shi ba.
Hukumomin Najeriya dai na ci gaba da musanta cewa jami’an tsaro sun buɗe wuta kan masu zanga-zangar lumana ta adawa da zargin cin zalin ƴan sanda ta EndSARs.
a shi ne zargin rashawa da ɗaya daga cikin ƴan majalisar Birtaniya ya yi wa tsohon shugaban sojan Najeriya Janar Yakubu Gowon da ya mulki Najeriya tsakanin 1966 zuwa 1975.
Majalisar Birtaniya ta yi zargin cewa, “Yakubu Gowon ya gudu zuwa Birtaniya, da kuɗin da aka wawushe daga Babban Bankin Najeriya.”
An yi ta yawo da bidiyon ɗan majalisar da ya yi zargin a shafukan sada zumunta musamman Twitter, inda kuma ya janyo muhawara tsakanin ƴan Najeriya – wasu na bayyana girman matsalar rashawa a Najeriya wasu kuma na musanta zargin da aka yi wa tsohon shugaban sojan na Najeriya.
Wasu kuma sun yi kira ga tsohon shugaban ya fito ya yi magana game da zargin.
@jeffphilips1 ya bayyana shakku game da zargin inda ya yi tambayar cewa”yaushe Gowon ya kwashi rabin kudin CBN zuwa Birtaniya? Ina fatan lauyoyinsa sun fara nazarin mayar da martani.”