TARABA MAJALISA NA NEMAN YIN FITO NA FITO DA BANGAREN SHARI’AR

Taraba: Majalisa Na Neman Yin Fito Na Fito Da Bangaren Shari’ar Najeriya

Daga Umar El-faruk

Wannan na zuwa ne baya da alkalin kotu dake shara’a a babban kotun tarayya dake Abuja babban birnin kasar ta bukaci shugaban Majalisar wakilan Najeriya Honorobul Femi Gbajabamila da ya dakatar da Honorobul Ibrahim Gambo Mubarak tare Kuma da gaggauta rantsar da Honorobul Garba Chedi Hamman Julde Wanda shi ne jam’iyyar APC ta baiwa tikitin tsayawa takara tun da fari a matsayin dan majalisar wakilan tarayya Mai wakilan mazabar Bali/Gassol dake jihar Taraba.

Sai dai Kuma bayan da Honorobul Garba Chedi ya shiga zabe aka fafata takara da Shi Kuma ya yi nasara a zaben 2019, Shi Honorobul Ibrahim Mubarak Gambo ya garzaya kotu inda ta karbi kujerar Majalisar wakilan tarayya ta Bali/Gassol ta bashi, lamarin da babbar kotun kasa dake zama a Abuja ta ce akwai gyara domin kuwa shi Honorobul Mubarak baima ko shiga zaben ba, nan ta ke Kuma kotun ta bada umurnin a maida ma Honorobul Garba Chede Hamman Julde da kujerarsa, Sai dai kuma Majalisar na jan kafa wajen aiwatar da wannan umurni lamarin da ya kai ga tuni Ministan shara’ar Najeriya Abubakar Malami ya akama Majalisar wakilan wasikar ganin ta bi umurnin kotu amma duk da haka ta yi buris da batun.

Idan dai za a iya tunawa a lokacin kakan zaben 2019 jam’iyyar APC ta baiwa wasu daga cikin yayanta tikitin tsayawa takara batare da anyi zaben fidda gwani ba. Wato (automatic ticket) a turance, sakamakon rawa da suka taka wajen kare martabar jam’iyyar, wanda Honorobul Garba Chede na daya daga cikin su.

Munyi kokarin jin ta bakin mutane biyun da suke kai ruwa rana amma lamarin ya ci tura

Yanzu dai kallo ya koma sama, domin kuwa wannan kai ruwa rana ya koma tsakanin ofishin ministan shara’a da Kuma kotun da yanke hukunci da Majalisa ne ake kai ruwa rana abunda yasa wadansu ke ganin tamkar Majalisar wakilan Najeriya na ja da bangaren shari’ar kasar.

Ana sa ran ranar 3, Ga watan Disabar nan za a koma zama kotu domin kawo karshen wannan takaddamar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *