DAN KWALLON KUNGIYAR REAL MADRID EDEN HAZARD YA JI RAUNI
Eden Hazard ya sake jin rauni a wasan da Alaves ta doke Real Madrid 2-1 har gida a daren Asabar.
Hazard wanda wasa uku kawai aka fara da shi a Laliga ta bana, an sauya shi minti 28 kacal da fara wasan bayan ya turguɗe ƙafa.
“Eden, ina fatan ‘yar bigewa ce kawai. Abin da ya faɗa mana kenan. ‘Yar bigewa ce, ba mai tsanani ba ne,” in ji koci Zinedine Zidane bayan shan kashin.
Lucas Perez ne ya fara jefa ƙwallo a ragar Madrid daga bugun finareti bayan ƙwallo ta taɓa hannun Nacho.
Daga baya Joselu ya ƙara ta biyu sakamakon kuskuren da Thibaut Courtois ya yi na ba shi ƙwallo a ƙafarsa kafin daga bisani Casemiro ya farke guda ɗaya.
Rashin nasara ta uku kenan da tawagar Zidane ta yi, abin da ya sa take a matsayi na huɗu da tazarar maki shida tsakaninta da Real Sociedad da kuma Atletico Madrid, jagororin teburin La Liga.
Wasa 27 kacal Hazard mai shekara 29 ya buga tun bayan komawarsa Real Madrid a 2019 kan kuɗi fan miliyan 150.