Fiye Da Mutum 110 Aka Kashe A Borno, Inji Majalisar
Majalisar dinkin duniya ta ce manoman shinkafa fiye da 110 Boko Haram ta kashe a ranar Asabar a kauyen Zabarmari dake karamar hukumar Jere a jihar Borno.Sanarwar ta fito ne daga bakin Edward Kallon, Kodinetan lura da jinkai na majalisar dinkin duniya a Nijeriya. Inda ya tabbatar da cewa; an kuma raunata da daman gaske a mummunan harin ta’addancin.