MANOMA 110 DA AKA KASHE A BARNO BA SU NEMI IZINI BA KAFIN SU JE GONAR -GARBA SHEHU

Manoma 110 Da Aka Kashe A Borno Ba Da Izini Suka Je Gonar Ba -Garba Shehu

 

Kakakin shugaban kasa Buhari, Garba Shehu ya ce manoman shinkafar da Boko Haram suka yi wa yankar rago a kauyen Zabarmari dake jihar Borno ba su nemi izinin rundunar sojin Nijeriya ba kafin su koma gonakinsu su fara ayyukansu.

Garba Shehu ya bayyana hakan ne ga ga BBC ‘Newsday’, inda ya ce gwamnatin ta yi bakin cikin abin da ya faru, sai dai ya ce; “amma ya kamata mutane su san me yake faruwa a yankin Lake Chad’.

Ya yi ikirarin cewa duk da mafi yawan yankin an kwace daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram, amma har yanzu akwai wuraren da ba a kai ga kammala kwacewa da har ‘yan kauyen da suke gudun hijira za su samu su koma.

“dole ne mu fadi gaskiya. Shin sojojin da suke kula da yankin sun ba su damar (zuwa gonakinsu)?” ya tambaya. Inda ya kara da cewa; “shin an ce ma wani ya koma wani aiki?”

Garba Shehu ya ce rundunar soji ta shaida masa cewa; ‘yan kauyen da aka yi wa yankar ragon ba su nemi izinin sojoji ba kafin su je gonakin na su, inda suka kai kansu ga mahallaka. “yankin da ‘yan ta’adda suka mamaye”. Inji shi.

Ya ci gaba da cewa; “a babin shawara irin wadannan wurare akwai bukatar a nemi izinin sojoji kafin a koma, ko kuma ma manoma su koma ayyukansu”. Ya tabbatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *