RASHIN TSARO – AL’UMMAN SUN CE “MUNA SON BUHARI YA SAUKA DAGA MULKIN NIJERIYA

Rashin tsaro: ‘Muna so Buhari ya sauka daga mulkin Najeriya’

‘Yan Najeriya da dama musamman a shafukan sada zumunta sun fusata, inda suke tattaunawa kan maudu’ai daban-daban inda suke nuna ɓacin ransu da kuma kira ga Shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya sauka.

‘Yan ƙasar dai sai sun fusata ne tun bayan da wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka kashe manoma 43, inda daga baya Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa mutum 110 aka kashe.

Hakan ya ja ‘yan Najeriya suka fitar da mau’du’ai daban-daban waɗanda suka haɗa da #BuhariMustGo da #BuhariResignNow, wanda hakan ke nufin Buhari ya sauka daga mulki, akwai kuma mau’du’in #SackTheServiceChiefs wwato a sallami shugabannin tsaron ƙasar.

Haka kuma akwai maudu’in da aka fito da shi na #EndNaijaKillings wato kawo ƙarshen kashe-kashen Najeriya, da kuma #ZabarmariMassacre wanda maudu’i ne da ke jaje ga manoman na garin Zabarmari da aka kashe a Bornon.

Duka waɗannan mau’du’an da ake tattaunawa sun samu karɓuwa a shafin Twitter inda mutane ke ci gaba da yaɗa su da rarraba su, kuma akasarin mutanen da ke waɗannan ƙorafe-ƙorafen suna nuna gazawar shugaban ƙasar da kuma neman ya sauka daga kan mulki.

Sai dai tun bayan wannan mummunan kisan da aka yi wa manoma a Borno, tuni mai magana da yawun shugaban ƙasar Garba Shehu, ya fitar da sanarwa inda ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya nuna damuwarsa matuƙa kan lamarin kuma yana bai wa sojoji gudunmawa kuma zai ci gaba da ba su gudunmawar domin samar da tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *