KAUNAR JUNA SHI ZAI TABBATAR DA ZAMAN LAFIYA A NIJERIYA
Inji Edwrd Kallon
Daga Zubairu M Lawal Lafia
Majalisar Xinkin Duniya da Gwamnatin tarayya da kungiyoyi masu zaman kansu sun dukufa wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin al’umman Nijeriya.
Babban kodineta na ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Nijeriya Mista Edward Kallon ya kasance jagaba wajen tuntubar al’umomin yan kunan Arewa Maso gabashin Nijeriya da yankin Arewa ta tsakiya domin samar da zaman lafiya a yan kunan.
Tawagar hadin giwar sun ya da zanga na farko a jihar Taraba inda suka samu goyon bayan kungiyar tallafin marasa galihu na Janaral T.Y.Danjuma suka gudanar da taron su a garin Takum cikin jihar Taraba.
Taron ya samu halartan masu ruwa da tsaki na kabilun dake Karamar Hukumar Takum maza da mata da mabiya addinai dabam dabam.Kabilu dabam dabam dake kan iyakar Kamaru da Nijeriya sun halarci taron domin bukatar zaman lafiya.
Har wayo tawagar ta isa garin Jalingo Babban birnin jihar Taraba inda ta shawarci al’umman jihar dasu zaman to masu hadin kai da yiwa juna uzuri.
Sannan su zaman to masu baiwa juna shawarwari da kaunar juna.domin shine jigon tabbatar da zaman lafiya. Tawagar ta isa zuwa jihar Plateau da jihar Yobe da Adamawa da jihar Borno.
Haka zalika sun ziyarci jihar Benue da jihar Nasarawa inda suka bukaci manoma da makiyaya su zaman to masu tattaunawa da juna dak guraren da tawagar ta zaga ta kwadai tar dasu hanyoyin da zasu bi domin zaman lafiya da juna.
Miste Edward Kallon ya janyo hankalin jama’a a guraren da suka zaga cewa su kasance tankar yan uwan juna da nuna kauna da juna da girmama juna wannane kadai hanyar zaman lafiya mai daurewa.
Ya qara da cewa hadin kai da zaman lafiya shine hanyar da zai bunkasa tattalin arziki a qasan nan . sai da zaman lafiya ake samun arziki.
Sai an yarda da juna da kaunar juna ake samun zaman lafiya da cigaban kowata al’umma.ya ce wannan itace hanya daya da zamu samu mafita.