KYAUTATAWA RAYUWAR TALAKAWA GWAMNA ABDULLAH SULE YA AZURTA WASU ZUWA JERUSALAM

KYAUTATAWA RAYUWAR TALAKAWA GWAMNA ABDULLAH SULE YA AZURTA WASU ZUWA JERUSALAM

Daga Zubairu M Lawal

Wasu kananan Ma’aikata da Allah ya tsaga da rabonsu kakarsu ta yanke saqa suka fuskanci abin mamaki da basu taba tunanin zai faru da su ba.

Ma’aikatan da suke aikin shara a gidan Gwamnatin jihar Nasarawa sun wayi gari cikin farin ciki da jindadin rayuwa mara iyaka.

Sakamokon jajircewar Fidelis da Maman Kingsley na zuwa aiki a kan lokaci sunyi karo da tagomishin dubun arziki daga Gwamna Abdullah Sule.

Inda ya tarar da su a bakin aikin su na shara babu kakkautawa Gwamnan ya dauko kujerar aikin ziyara zuwa Jerusalem ya ba kowa daya daya.

Wannan goma ta arziki da Gwamnan yayi ma kananan Ma’aikatan ya sanya jama’a da dama firin ciki da yabawa da ayyukan alheri da tausayi irin na Gwamna Abdullah Sule

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *