KO KUNSAN CEWA – NI NA DAUKI MATASAN JIHAR NASARAWA A MATSAYIN YA’YAN CIKINA NE – SILIFAT A.A.SULE

KO KUNSAN CEWA – NI NA DAUKI MATASAN JIHAR NASARAWA A MATSAYIN YA’YAN CIKINA NE – SILIFAT A.A.SULE

Daga Zubairu M Lawal

Uwar gidan Gwamnar jihar Nasarawa, Giwan Matan Nasarawa Hajiya Silifat Abdullahi Sule ta nuna goyon bayanta ga matasan jihar, a inda ta bayyana cewa ita Uwa ce a garesu, kuma duk wani goyon baya da ya kamata ta basu za su samu daga gareta.

Uwargidan Gwamnan Hajiya Silifat Abdullah Sule ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke jawabi a wajen taron matasa da ya gudana a fadar Filin wasa ta garin Gudi dake karamar Hukumar Akwanga cikin jihar Nasarawa.

Taron da matasan garin Gudi suka shirya domin cigaban matasa da Kuma yankin Gudi.(Gudi Youth Progressive and Development Association).

Hajiya Silifat Abdullah Sule tace ita Uwa ce ga dukkanin matasan jihar Nasarawa kuma tana baiwa matasa tallafi a harkokin cigaba yadda ya kamata.

Ta dauki rayuwar ta wajen cigaban matasan jihar Nasarawa saboda taga cigaban jihar da bunkasa tattalin arziki jihar Nasarawa.

Hajiya Silifata ta ce tana alfahari da matasan jihar Nasarawa saboda yadda suke kokarin ganin cigaban jihar Nasarawa.

Hajiya Silifata ta kara kira ga Matasan jihar Nasarawa da su kara kaimi wajen tsayuwa da kafafun su domin cigaban jihar Nasarawa. Wajen kirkirar abubuwan cigaba da dogaro da sana’o’in hannu domin habbaka jihar Nasarawa a fannin tattalin arziki.

Uwargidan Gwamnan ta shawarci matasan jihar Nasarawa da su guji ta’amali da miyagun kwayoyi da harkon shaye-shaye saboda babu cigaba face jefa kai cikin hadari.

Da yake jawabi a wajen taron Shugaban  kungiyar cigaban matasan garin Gudi Ezekiel Mathias ya bayyana Uwargidan Gwamna Hajiya Silifat Abdullah Sule da suna Maman Matasan Gudi.

Saboda duk gudumawa da kulawar da ya dace Uwa ta baiwa ya’yan ta Hajiya Silifat ta baiwa matasa.

Ya qara da cewa ya’yan kungiyar ( Gudi Youth Progressive and Development Association) ba zasu manta da Uwargidan Gwamnan ba saboda yadda take yaki da masu cin zarafin mata da yara kanana.

Ya ce , zuwan Gwamnatin Injiniya Abdullah Sule tare da Hajiya Silifat mata da matasa sun amfana da tallafi na cigaba da harkokin Sana’a dabam dabam.

Mista Ezekiel Mathias ya kara kira ga matasa dasu zamo tsintsiya madaurinki daya su bada kai domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban jihar Nasarawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *