GWAMNA ABDULLAH SULE YA JAJANTAWA IYALAN HABU GALADIMA
Daga Zubairu M Lawal
Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya yayantawa iyalan Farfesa Habu Galadima Babban Darkta a Ma’aikatar Gidauniyar Ilumin tsaretsare ta kasa (DIRECTOR GENERAL, NATIONAL INSTITUTE FOR POLICY AND STRATEGIC STUDIES).
Marigayin Dan Asilin jihar Nasarawa ne wanda ya rasu a jiya. Gwamna Abdullah Sule ya nuna alheni da wannan babban rashi da akayi.
Ya qara da cewa wannan babban rashi ba al’umman jihar Nasarawa kadai akyiwa ba ya shafi al’umman Nijeriya ba ki daya.
Saboda Farfesa Habu Galadima hazikine da dubban al’umma suke karuwa da shi. Samun cike gurbinshi sai anyi da gaske.
A takardan da Babban hadimin Gwamna Abdullah Sule a fannin yada labarai ya rubuta Malam Ibrahim Addra. Ya ce Rasuwar Habu Galadima ta kiddima al’umman jihar Nasarawa.
Kuma yqyi kira ga iyalqn Farfesa da su kara hakuri su cigaba da yimasa adu’a domin samun Rahamar Ubangiji.