KO KUNSAN – Yadda Talauci ke hana wasu yara mata karatu a arewacin Nijeriya?

Yadda Talauci ke hana wasu yara mata karatu a arewacin Nijeriya

Inji Farida Adamu

Daga Zubairu Lawal

A wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar ta tattauna da wata mata da ta sheda cewa talauci ke dakushe karatun mata a Arewacin Najeriya.

Wata mata mai suna Farida Adamu wacce take zaune a jihar Kebbi, kuma mujin ta ya mutu ya bar mata yara,  ta nuna cewa talauci ne ya dakushe  karatun ‘ya’ya mata.

Ta bayyana cewa ‘yar ta ta fari ta yi aure ba tare da ta sami ilimin zamani ba. Ita kuma daya ‘yar ta ta yanzu haka Makarantar Islamiyya kawai take iya zuwa saboda rashin kudi.

Farida Bazaurace wanda take zaune a garin Kawara-manu  mijinta ya mutu ya barta da yara biyar ita take kula da cinsu da shansu.

Farida tana da qananan yara guda uku Wanda yanzu haka basu iya zuwa makarantar Boko sakamakon kasuwancin da take yi bai taka kara ya karya ba.

Farida ta bayyana cewa koda zata iya sanya yaranta mata a makaranta dole tana bukatar #24,000 da zata saya masu kayan makaranta da kuma abinci da zasu rika ci a duk lokaci.

Binciken ya nuna cewa Nijeriya ce kasar da ilu!im yara kananan yake koma baya. Ana kiyasta cewa akwai yara sama da miliyon 13.5  da basu zuwa makarantu sakamakon matsalolin rayuwa.

Yanki  Birnin Kebbi da Sokoto da Zamfara da Katsina lamarin yana kara zurfafa rashin samun ilumin yara mata masamman a yana yin da yanzu kasar ke ciki.

Kimanin yaran da a yanzu suka rasa matsugunai a kauyukansu sun haura 501,574.

Hukumar kula da yara qanana na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ta nuna damuwa da halin da yara kanana ke fuskanta na rashin samun karatu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *