Saboda murnar shiga shekarar 2021 Uwargidan Gwamnan Nasarawa tayiwa Sabin Jarirai Goma ta arziki

Silifat ta rabawa jarirai gudumawar saboda murnar shiga shekarar 2021 a Nasarawa

Daga Zubairu M Lawal

Uwargidan Gwamnan Jihar Nasarawa Hajiya Silifat Abdullah Sule ta rabawa jarirai sabbin haihuwa kayan tallafi saboda murnar shiga sabuwar shekarar 2021

A ranar juma’a 1/1/2021 da misalin karfi daya na rana Uwargidan Gwamnan Hajiya Silifat Abdullah Sule ta isa Babban Asibitin dake garin Lafia wato Dalhatu Araf.

Inda ta gewaya daken da ake kwantar da jarirai sabobin haihuwa tare da iyayensu tayi masu tukuci saboda murnar shiga sabuwar shekara da ya fado a ranar juma’a.

Hajiya SILIFAT ta fara ne da Uwargidan Alhaji Garba Arikya wanda matarsa ta haihu ya mace, bayan bata gudumawar ta kuma nuna godiyarta da yadda iyayen yarin yan suka bukaci sanyawa jaririyar suna Silifat.

Cikin tawagar nata akwai Uwargidan Mataimakin Gwamna Misi Shola Tosan Akabe da kwamishiniyar Ilumi Hajiya Fati Sabo Jimita da kwamishiniyar harkokin mata da walwala Hajiya Halima Ahmad Jabiru.

Da Uwargidan Shugaban karamar Hukumar Lafia da sauran matan Kwamishinoni da masu rike da mukaman siyasa.

Barinta Asibitin Dalhatu Araf ta garzaya zuwa Asibitin sha ka tafi dake kwandare da Asibitin garin Nasarawan Eggon inda ta rarrabawa sabobin jarirai gudumawar murnar shiga sabuwar shekara 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *