MASU GARKUWA DA MUTANI SUN SACE MUTUM 20 SUN KA SHE DAYA A NASARAWA

MASU GARKUWA DA MUTANI SUN SACE MUTUM 20 SUN KA SHE DAYA A NASARAWA

Gungun yan Ta’adda dake dauke da miyagun makamai sun addabi al’umman a yan kin Karamar Hukumar Toto dake jihar Nasarawa sun kashe mutum daya sun kumayi Garkuwa da mutum 20.

Mutanin da yan Ta’addan suka far masu matafiyane wadanda ke kan hanyar zuwa  Nasarawa dsgaToto. yan Ta’addan sun tsare hanyar Buga-Gwari da ya hada Gadabuke a kan hanayr Toto.

Lamarin ya faru ne a daren Littinin misalin 6:30pm zuwa 7:pm yan ta’addan sunyi ta harbi kan mai uwa da wabi idan nan take suka tsai da duk wani mota dake zuwa.

Sun kuma tafi da mutanin da suka sace a nan ne suka kashe mutum daya mai suna Malam Silihu suka jefar da gawar.

Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da faruwan lamarin a ta bakin jami’in hulda da jama’a na Rundunar Mista Ramham Nelson ya sheda wa manema labarai cewa abin ya farune a cikin daren Kuma Rundunar yan Sanda sun kai dauki amma sun tarar da mota daya ne mai lamba  NTT 265 AA.

Amma basu da labarin adadin mutanin da aka sace. Kwamishinan yan Sandan jihar Nasarawa Bola Longe ya ummurci DPO da ya dauki motar da a ka gani a wajen zuwa ofishin yan Sanda dake Toto.

Shugaban karamar Hukumar Toto Hon.Nuhu Adamu Dauda ya sheda faruwan lamarin. Idan ya tabbatar da cewa an sanar da shi cewa yan Bindiga sun kashe mutum daya kuma sun yi Garkuwa da wasu .

Ya ce mun tura Rundunar yan Sintiri sun shiga dajin inda suka tarar da gawan wani mutum daya a kusa da kauyen Gubasa.

Sun daukoshi an tabbatar da wadanda suka sanshi Malamin Makaranta ne a yanzu, a baya jami’in Hukumar zave ne a jihar Nasarawa.

Shugaban karamar Hukumar ya ce har yanzu yan sintirin suna daji suna bincikawa ko Allah zai sa a gano mutanin da Kuma mabuyar yan Ta’addan.

Sannan yayi kira ga al’umman yankin Toto dasu rika bayyanawa jami’an tsaro duk Wanda suka san yana aikata ire-iren wannan aiki ko makqmancin sa, ko kuma wanda suka gani basu amince da take taken sa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *