Bankin Duniya zatayiwa gidaje 50,000 ridista kyauta a Nasarawa

Bankin Duniya zatayiwa gidaje ,50,000 ridista kyauta a Nasarawa

Daga Zubairu M Lawal

Hukumar Bankin Duniya ta fito da tsarin tallafi ga marasa galihu a Qananan hukumomi shida  a jihar Nasarawa inda ta dauki nayin yiwa Gidaje kimanin 50,000 cijin gundumomi 24 a jihar.

Cikin Kananan hukumomi da za a gudanar da wannan tsarin takardan gidaje sun hada da karamar Hukumar Lafia inda aka zave gudumomi hudu a cikin Karamar Hukumar Lafia.

Suna hada da Gundumar Ciroma da Gudumar Zanwa da Gayam da kuma Makama.

Da yake jawabi Kwamishinan harkokin kudi ta jihar Nasarawa Honorabul Haruna Adamu yace aka sarin gidaje basu da tsarin nombobi na zamani.

Akan hakane Bankin Duniya ta kuddurin aniyar tallafawa wasu gidajen a fadin tarayyar Nijeriya ciki harda jihar Nasarawa saboda su samu maki da tsarin takardun gidaje na hukuma.

Yace jihar Nasarawa ta tanadar da cibiyar tasiwurar gidaje da yadda za a yi masu ridasta amma mutani da dama basu iyayi saboda matsalar kudi.

Yace wannan Ridistan yana taimakawa masu gidaje saboda koda wani rikici ya taso akan gida da zarar akaje NAGIS aka duba taswurar gidaje za a ga gidanka da sunan mai gidan da nombar gidan.

Qaramar Hukumar Lafia wanda Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Aminu Ma’azu Maifata ya jagoranci zaman tattaunawar ya bukaci al’umman Karamar Hukumar Lafia da su ka kasance cikin Gundumar da ta samu wannan tallafin da su baiwa Ma’aikatan hadin kai saboda wannan tallafi ne mai kyau wanda zai amfani duk magidanci da gidansa ya samu wannan ridista.

Kuma wannan ridistan kyautane babu bukatar wani yace ba zaiyi ba saboda babu kudi.

Shugaban Qaramar Hukumar Lafia wanda Sakataren Qaramar Hukumar ya wakilta ya qara janyo hankalin mahalarta taron da su fadakar da jama’an ungunwansu da su baiwa Ma’aikatan hadin kai su bude baki su amsa tambayoyi a lokacin da ake gudanar da tsarin yadda za a yiwa gida ridistan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *