Ya kamata a habbaka hanyoyin samar da abinci a Nijeriya
Inji Osinbajo
Daga Zubairu M Lawal
Mataimakain shugaban kasar Najeriya, mista Yemi Osinbajo ya bada shawara da cewa ya kamata a habbaka harkokin noma ko kawo tsarin abinci mai gina jiki ga kasa.
Yace idan akayi la’akari ga yadda ake samun karuwan mutane a kasar wanda zai iya janyowa qasar matsala nan gaba ta fuskar tattalin arziki.
Akwai alamar tambaya ta vangaren sarrafa abubuwa da qasar keyi da kuma kirkirar samar da aikinyi da kuma yadda ake gudanar da rayuwa na yau da kullum kuma yadda ake gina hanyoyi na samar da abinci harma da kiwon lafiya.
“Mataimakin shugaban kasa yayi bayani kan abincin da muke samarwa wanda muke ci ya zama kowa zai iya sanya kudi ya saya ba wanda zai kawo matsalolin da zai gagari talaka ba”. Inji shi.
Mataimakin Shugaban qasa yayi wannan jawabine a yayin taron majalisar dinkin duniya kan yadda za’a fidda tsarin abinci wanda aka gudanar tsakanin Gwamantin Najeriya tare da hadin gwiwar majalisar dinkin duniya da aka gudanar wanda ya samu halartar sama da mutane dari bakwai (700).
Mataimakin shugaban Nijeriya ya kara da cewa samar da tsarin abinci wanda zai yi aiki ba abune dake bukatar hanzari ba, da kuma sauri duba da yadda talauci ke kara kamari musamman lokacin cutar ‘korona bairos’ da kuma faduwar tattalin arziki.
A wani karin bayani kuma da ministan kudi da tsare tsare da kuma tsarin yadda za’a kashe kudin Hajiya Zainab Ahmed, tace Gwamnatin Najeriya ta nuna kokarinta wajen ganin ta kawo karshen yunwa a shekarun baya ta hanyar kawo noma da kuma cin abinda aka noma wanda shine zai kawo dogaro da abin da yan kasa suka noma ko kuma aka sana’antar.
A nasa jawabin Babban Kodinata na Harkokin Majalisar Dinkin Duniya Mista Edward Kallon ya yabawa gwamnatin Najerya na yadda zata kawo tsarin abinci da kuma nada ministan kudi ta jagoranci wannan tafiyar.