ZIDANE YANA SHIRIN BARIN AIKI A QUNGIYAR REAL MADRID
Daga Amina Sani
Zinedine Zidane ya nuna cewa, ya gaji da zama a Real Madrid. Inda kuma yace, “A shirye nake na sauka daga matsayin mai horar da ‘yan wasan kungiyar ta Sifen a karshen shekarar 2020-21”.
In ba a manta ba Zidane din yana da kwantaragi da bai gama ba a Bernabeu har sai zuwa watan Yuni mai zuwa, amma wasu da yawa daga yan wasan sa suma sun nuna soyuwarsu da barinsa aiki a wannan qungiya.
Wasu na zargin cewa ko hakan yana da nasaba da warwasa qungiyar Madrid din da akai ne, a gasar cin Kofin Zakarun Turai a matakin kusa da karshe da suka buga da qungiyar ƙwallon kafa ya Chelsea ya jawo haka wanda aka taka wasar a daren Laraban nan data gabata.