Sen. Shehu Sani ya nuna damuwa da yadda matasa ke tada hankali kan wasan ƙwallon Man City da Chelsea, amma basu damuwa da ƙwallon gida Najeriya.
Daga Zubairu M Lawal
A yau asabar ne yayin da ake tunkarar buga zazzafan wasan Man City da qungiyar kwallon ƙafa ta Chelsea, Sanata Garba Sani, ya koka bisa kan rashin damuwa sa wassanin kwallon kafa da ake bugawa a gisa Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na twitter, inda yake cewa; “A yau, Jigawa Golden Stars za ta buga wasa da Lobi Stars a Kaduna, amma mutane suna magana ne kawai game buga wasan Man City da Chelsea; dole ne Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya ta yi aiki tukuru don sauya wannan tunanin.” Inji shi.
Hakika wannan kalubale ne ga matasanmu, masu ra’ayin kallo da buga kwallon kafa. Don yana da kyau duk wani san kasa ya zama mai kishin kasar sa, hakan zai bawa mutane da yan wasanmu karfin guiwa yayin tunkarar cin nasara a wasan kwallayensu.