KO KUNGA – Yadda aka gudanar da bukin Sallah a Fadar Sarkin Lafia

KO KUNGA – Yadda aka gudanar da bukin Sallah a Fadar Sarkin Lafia

Daga Zubairu M Lawal

Bayan kammala Sallar Idi Karama Babban Masallacin Idi dake kan titin shandan cikin garin Lafia.

dubban Jama’a sukayi chachirido karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukuma Lafia Kuma Jagoran Chiyamomin Jihar Nasarawa Alahaji Aminu Ma’azu Maifata.

Inda sukayiwa Sardaunan Gwandran Nijeriya Sanata Alhaji Umar Tanko Al-makura rakiya zuwa fadan Maimartaba Sarkin Lafia Kuma Shugaban Majalisar Sarakunaa ta jihar Nasarawa, Mai Shari’a Muhammad Dauda Sidi Bage.

Tawagar ta isar da gaisuwar Sallah da nuna godiya da yadda masarautar ke tafiyar da al’amurar al’umman jihar cikin kauna da kyautatawa.

An kuma gudanar da shagulgula da nuna kaunar juna da girmamawa. An kuma taya juna murna da yin fatan alheri, Sarkin Lafia Mai shari’a Sidi Bage ya nuna godiya da wannan ziyara ta Bangirma.

Dubban mutani suna nuna godiya da sa albarka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *