SAKON GWAMNA ABDULLAHI SULE – Da ilumi zamu kawar da Bangar siyasa a jihar Nasarawa

Da ilumi zamu kawar da Bangar siyasa a jihar Nasarawa
– Gwamna Abdullah Sule

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya bayyana hakane a lokacin da yake jawabi gaban dubban al’umman Karamar hukumar Toto dake jihar Nasarawa.

Gwamnan yace na saurari bayanan kowa daga cikinku dama makasudin zuwanmu nan shine muji damuwarku daga bakinku Kuma mun saurari matsalolin ku.

Gwamnan yace; samar da manyan makarantu na gaba da Sakondire a yankin Karamar hukumar Toto zai kara baiwa matasa damar samun ingantaciyar Ilumi da zai wayar masu dakai saboda su dogara da kansu da kuma sana’o’in da sukeyi.

Gwamna Abdullah Sule yace; burin Gwamnatinsa sanya al’umman jihar Nasarawa akan hanya mai daidai ciya da zata kaisu ga cigaba koman daren dadewa.

Gwamnan ya qara da cewa batun harkan tsaro “na gode maku da kuka yaba da kokarin da mukayi maku. Ina mai tabbatar maku nan da kwanaki kankani zakuga gamayyar jami’an tsaro zasu shiga dazukanku su farauto yan Ta’addan da suka kutso suka shigo suke barna.

Mun tattauna da Rundunar 177 da sauran bangarorin jami’an tsaro lokaci kawai ake jira.

Kun tabbata a lokacin da mukazo Gwamnati akwai matsalar tsaro saboda yan Kungiyar Darul-Salam da a shekarar 2007 – 2008 suke gudanar da ayyukansu a dajin Nije, bayan tarwatsasu sun dawo dajin Toto mukayi amfani da jami’an tsaro na musamman suka kamo sama da mutum 1000 maza da mata da yara”.

Gwamna Abdullah Sule ya yi kira ga al’umman yankin Qaramar Hukuma Toto da su zama masu kaunar juna su zauna lafiya da dukkanin kabilun da suke rayuwa tsakaninsu.

Yace; sai da zaman lafiya da hadin kai za a samu biyan bukata. Amma idan gida babu zaman lafiya babu hadin kai makiya suna samun dama su farmakesu.

Tunda farko Jama’a da dama maza da mata sun bayyana bukatunsu a gaban Gwamna da tawagarsa. Sun kuma yabawa Gwamnan kan kokarin da yayi na maido da zaman lafiya a wannan Karamar Hukuma ta Toto.

Sun tabbatar da kafin zuwansa Gwamna Karamar Hukumar bata shiguwa saboda matsalolin waje da cikin gida da suka addabi Jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *