Yanwasa Guda 2 Manchester City Tasa Agaba Domin Sayensu

Yanwasa Guda 2 Manchester City Tasa Agaba Domin Sayensu

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta bayyana cewar babu abin da yake a gabanta sai ‘yanwasa guda biyu da zata saya domin kawosu ƙungiyar.

Hakan na zuwa ne biyo bayan yadda ƙungiyar ta City take sake ɗaura ɗamara domin tunkarar sabuwar kakar wasa ta bana da za a fara a watan gobe na Ogusta.

Manchester City dai na yunƙurin kawo shararraen ɗanwasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham kuma jagoran ‘yan wasan ƙasar Ingila wato Harry Kane a matsayin wanda zai maye gurbin Kun Aguero Sergio wanda ya koma Barcelona.

Haka zalika Manchester City ta matsa ƙaimi wajen sayen Jack Grealish zuwa ƙungiyar domin yin garambawul musamman a tsakiyar ƙungiyar.

Manchester City dai tasha kaye a wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai a kakar wasan data gabata bayan da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta wanke ta daci 1 mai ban haushi kuma tayi awon gaba da kofin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *