Kungiyar JNI da CAN reshen jihar Nasarawa sunyi Sun nuna damuwa da abinda ke faruwa a Plateau
Daga Zubairu M Lawal Lafia
Kungiyar Musulmai na (JNI) ta kasa Reshen jihar Nasarawa da takwararta kungiyar Kiristoci (CAN) ta kasa reshen jihar Nasarawa sun nuna damuwa da bakin ciki ga abinda ke faruwa a makwaftarsu ta jihar Plateau.
Shugabannin kungiyoyin addinan sun fitar da sanarwan nuna damuwa da jimami ga abinda kefaruwa a jihar Plateau na kisankai mara dalili.
Jagororin kungiyar sun fitar da sanarwa ne bayan kammala wani tattanauwa a ranar alhamis 19/8/2021 inda suka rabawa manema labarai a garin Lafia.
Da yake zantawa da manema labarai Imam Muhammad Ali da yafito daga bangaren (JNI) ya nuna damuwa da abinda yajanyo asarar rayuka a jihar Plateau, wanda ta kai yanzu miliyoyin Jama’a na cikin kuncin rayuwa.
Imam Muhammad Ali yace, Allah ya la’anci mai tada fitina saboda idan fitinar tazo ba guri daya zata tsaya ba.
Sannan yayi kira ga al’umman jihar Plateau su kara hakuri, su kaunaci junansu shine hakikanin zaman lafiya.
Ya Kuma ummuci dasu kiyaye dokokin da Gwamnatin jihar Plateau ta gindaya domin kara samar da zaman lafiya mai dorewa.
Imam Muhammad Ali yace matsayin kungiyoyin addinai a jihar Nasarawa ya zo daya inda suka nuna damuwa da kisan gillar da akayiwa matafiya a jihar Plateau Wanda ya janyo tashin hankali.
Sannan Gwamnatin jihar Nasarawa tana kira ga al’umman jihar Plateau sun rungumi akidar zaman lafiya da juna domin shine zai kai jihar zuwa ga turban cigaba mai dorewa.