Hadin giwa da kamfanonin da zasu kula da Na’urorin jinya a Asibitin DASH, zai kawo cigaban kiwon lafiya a Nasarawa
Daga Zubairu M Lawal Lafia
Sanannen abune cewa Gwamnatin jihar Nasarawa ta kashe miliyoyin nairori wajen sayo Na’urorin jinya da aka sanya a Asibitin Dalhatu Araf DASH dake Lafia, domin inganta harkan kiwon lafiya a jihar Nasarawa.
Duk da cewa Gwamnatin tayi haka domin taimakawa al’umman jihar Nasarawa da kasa baki daya da kuma samar da kudaden shiga.
Amma ana samun rashin kulawa daga wasu janibin Likitocin dake amfani da wasu Na’urar, basu ba da kulawa ya sanya Na’urar duk da Ingancinta amma bata karko.
Shugaban Asibitin Dalhatu Araf Dakta Ikrama Hasan kwarare kuma masani a kan harkan kiwon lafiya ya ya bayyana cewa matukar ana son ganin ingancin wadannan Na’urorin da Asibitin kwararru na Dalhatu Araf dake Garin Lafiya ke amfani dashi ya cigaba dole a sanya hannu cikin wani yarjejeniya kamar yadda wasu manyan asibitin koyarwa keyi a kasan nan.
Yin amfani da hadin gwiwar kungiyar ‘Muliti million naira city scan machine’ wanda Gwamnatin Nasarawa ke lura dasu cigaba ne so sai.
Ya kuma ce wannan yarjejeniya wanda yana gaban Gwamnan, Engineer Abdullahi Sule shine kadai zai bada dama a aiwatar da yarjejeniyar ” multi million naira city” wanda za’a kawo sababbin kayayyakin aiki da masu iya sarrafasu.
Yace; kudi da Gwamnati ta ware ta sayo Na’urorin T.C.Scan naira million dari uku 3,000,000 bai kamata ace munyi sakaci wannan Na’urar an barshi ya lalace a banza ba.
Na’urace da ke bayyana duk wani cuta dake jikin mutum a sa’ilin da ya kwanta yin gwaji. Hakan yasa muke bada shawara kan wanda zasu lura dashi sune kwararun kamfanoni masu zaman kansu. Inda zasu iya baiwa Asibitin kaso 80% ko 90% su kuma su tafi da kaso 10% ko 20%.
Ya kara da cewa a wasu Asibitocin dake da wannan Na’urorin na( T.C Scan)marasa lafiya suna biyan kudi mai yawa amma a DASH zasu biya kudi daga naira dubu 60 zuwa dubu 70 wannan kuma saukine mai yawa.
Sabo da rashin kyakyawar kulawa da wasu Likitocin ke baiwa kayan Gwamnati akwaii sabon kayan aikin gwaje gwaje wanda Gwamnatin Nasarawa suka sanya yanzu sun tsaya da aiki.
Ya qara da cewa; PPP sune wanda zasu tallata abubuwan kuma sune zasu shiga gidajen radio su fadi sababbin kayan aiki a ma’aikatan kwararru dake lafiya.
Ganin haka ya sanya muke ganin ya kamata Gwamnatin Nasarawa ta sanya dokar hukunta duk wadanda suke aiki a bangaren Na’urorin idan sukayi sakaci, ko kuma dankashi a hannun Kamfanoni masu zaman kansu da zasu rika gudanar da ayyukan kiwon lafiya a cikin Asibitin.
Sakacin da akayi shine yasa sabbin kayan aiki da aka siyo dake asibitai basa aiki yadda ya kamata saboda ba’a kula dasu yadda ya kamata kuma Daktocin basa lura dasu duk da cewa ana biyansu kudi mai yawa.
Duk da haka al’umma a waje suna zargi likitocin dake aiki a asibitin DASH sunada wani halayya na karkatar da marasa lafiya zuwa asibiticinsu na musamman domin yi musu aiki ko kuma kula dasu.
Duk da cewa an kai korafi ga Shugaban Asibitin mai suna Dr. Ikrama Hassan da kuma matakan da za’a dauka akan irin wayannan likitocin, abubuwan sai Kara ta’azzara yakeyi duba da kudin da ake samu a asibitin.
Wani majiya ya wallafa cewa daktoci a DASH musamman wayanda suke aiki a dakin gwaje gwaje sunada wani yarjejeniya da wasu a wajen Asibitin gurin gwaje gwaje wanda na’urarsu basa fitar da sakamako mai kyau.
saboda irin hakane , asibiti masu Zaman kansu da kuma manyan asibitai a fadin jihar Nasarawa sun nuna damuwarsu matuka saboda wasu asibitin gwaje gwaje suna karbar naira dubu 3 wasu kuma suna karbar naira dubu 2 kan Scan mai juna biyu ko makamancinsa, maimakon Asibitin DASH mai farashi #500.
Dakta Ikrama Hasan ya bayyana takaicinsa kan yadda ake samun wasu Likitoci da irin wannan muguwar dabi’a na tsanani ga al’umma wanda ya sabawa dokar aikin jinya.
Ya kara da cewa bayan samun wadannan korafe, korafen mun samu wani Likita da wannan aikin kuma mun dauki matakin dakatarwa a kansa.
Shugaban yayin dayake bayani kan sabbin kayan aiki yabada tabbacin cewa sabbin Na’urorin gwaje gwajen zaayi aiki dasu daga watan satumba na 2021 kuma yace a shirye suke a fara aiki.
Tsare-tsaren da muke a Asibitin shine muna kaddamar da bincike kan kayan aiki, wasu asibitin koyarwa kamar Federal medical centres dake keffi suna karban naira dubu 60 zuwa dubu 70, yace mu kuma zamu dinga karbar dubu 40 ko kuma fiye da haka saboda munada motar daukar Mara lafiya da kuma saukaka masu.
Dakta Ikrama Hasan yace; duk da cewa ya zuwa yanzu ana samun matsalar wutan Lantarki sakamakon lalacewar Injin Tiranfoma ta sanadiyar tsawan ruwan sama. Mum yanke shawarar yin amfani da wutan Janareta na awa 24 a bangaren Yara yan Bakwaini da ake sanyawa a Kwalba.
Duk da cewa bangarensu jinya kyautane, ta nan zamufi basu wutan Jannareta inda sauran gidajen Ma’aikata zasu rika samun wuta na awanni, domin babu isashen kudin sayan mai.