BINCIKE DA MATAKIN JUYI YA KAMATA A KAWO A KUNGIYAR KWALLON NASARAWA UNITED
Daga Zubairu M Lawal Lafia
Bai kamata Gwamnatin jihar Nasarawa ta zura ido tana kallon yadda ake gudanar da harkan wasan kwallon kafa a kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United ba.
Kungiyar tana mai taka mahimmiyar rawa da samu goyon bayan dubban mutani a jihar.
Kuma duk Gwamnan da ya rungumi harkan kwallon kafa yana samun goyon bayan al’umman masamman matasa maza da mata.
A shekarar mulkin Gwamna Abdullah Adamu ya samu goyon baya sosai a ciki da wajen jihar Nasarawa saboda yadda ya nuna kauna ga harkan wasanni a jihar.
A kakar wasa ta shekarar 2020 da 2021 Gwamna Abdullah Sule ya fara samun farin jinin matasa saboda yadda yake nuna kauna ga kungiyar Nasarawa United kuma yana biya masu bukata daidan Gwargwado.
An samu gagarumin nasara a harkan wasan kwallon kafa a lokacin Gwamnatin Injiniya Abdullah Sule saboda kungiyar tayi nasarar daukar Kofin kalubale a gasar da aka buga a birnin Kano.
Wannan shine nasara mafi girma a tarihi da kungiyar ta samu tsawan shekara 22.
Kwamishinan harkokin wasanni na jihar Nasarawa Malam Othman Bala Adam, ya kawo sauye sauye na cigaba a cikin harkokin wasanni a jihar.
Ya kuma dakile wasu hanyoyin musgunawa ko makamancin haka.
Abinda nake bukatar nunawa Gwamnatin jihar Nasarawa shine. Lokacin da Jama’a suke son ka ka sosu. Kuma dadewa a waje daya ba shine gogewa ba.
Kungiyoyin kasashen Turai suna iya sauya Shugabannin kungiyoyin su, matukar suka kasa tabuka komai.
A haka nake ganin ya kamata Gwamnatin jihar Nasarawa tayi koyi da takwararta ta jihar Kano.
A shekaran jiya Gwamnatin jihar Nasarawa ta dakatar da Ibrahim A. Musa.
Ba wai domin rashin gogewansa bane, a a kwararene. Amma ya kasa kaita ga matakin da take bukata.
Idan Gwamnatin jihar Kano da kungiyar Kwallon Kano Pillars take mataki na hudu a tsawan watani daga karshe ta koma na bakwai zata sallami mai horarwa, ina kuma ga Nasarawa United dake mataki na biyu, daga karshe a wasa daya ta koma na 6.
Rashin tabuka komai a kakar wasa ta 2020 da 2021 bai kamata ace Shugaban kungiyar Nasarawa United Mr.Isaa DanLadi yana zaune a wannan kungiyar ba.
Mafi mutumci a gareshi ya ajiye aikin saboda damar da ya samu guda uku ya kasa cin nasara a ko daya, abin kunyane ga kowani irin Shugaba.
1, tsawan watanni Nasarawa United tana mataki na biyu
Tana fatan haurawa ta daya, ko ta zauna a na biyun domin samun damar zuwa gasar zakarun nahiyar Afirka( African Champions League.
2, idan wannan damar bai samu ba Nasarawa United ta tsaya a gasar Continental.
3, Nasarawa United tana da dama guda biyu shen a matsayinta da take mataki na biyu wasa daya ya rage, sannan ga Babban dama zata buga wasan karshe na aiteu cup.
Ya kamata Gwamnati ta kafa kwamitin ta yaya akayi damar uku suka gujewa Nasarawa United bata samu kodaya ba.
Kuma yaya akayi babban rashin nasara a wasanta na karshe da kungiyar Abia.
Zamu cigaba , wajen bayyana irin kudaden da Gwamnatin jihar Nasarawa ta kashe a kakar wasa ta 2020/2021 , riba aka samu ko asara?