RAN MAZA YA BACI – SARKIN ZURU ZAI SANYA KAKI DOMIN FATATAKAR YAN TA’DDA A DAJI

KU KARANTA – ZAN SANYA KAKI DOMIN SHIGA DAJI YAKI DA YAN TA’ADDA – Sarkin Zuru

Sarkin Zuru, Rtd. Manjo Janaral Muhammadu Sani Sami (Sami Gomo II) yace ya fadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a shirye yake ya mayar da kakinsa ya kwashi kayan aiki su shiga fagen daga domin kawo karshen ta’addanci dake addabar kasarnan.

Sani Sami shi ya jagoranci mafi yawan yakukuwan da aka yi a zamanin baya kuma yayi nasara duka, ciki har da lokacinda aka kashe Murtala shine wanda ya gaggauta dakile juyim mulki da su Dumka suka so yi. Sannan shi ne ya jagoranci shirin ko ta kwana na yakin da aka so yi tsakanin Nigeria da jamhuriyar Kamaru, har wayau shine ya dauki fansa kuma ya fatattaki kasar Chadi har ya kama jiragen ta lokacin da ta kashe sojojin Nigeria.

Yace ko a shekarun baya ma kishin kasa yasa suka jajurce domin ganin Nigeria ta zama kasa daya dunkulalliya.

Yace sha’anin tsaro abu ne da ya shafi kowa da kowa ba shugaban kasa kadai ba, “Ni a masarautar Zuru na kafa kwamiti mai karfi kan sha’anin tsaro sannan mun baiwa Gwamnati shawara kuma mun koma bin tsarin da, ko bako yazo gidan mutum sai mai unguwa ya sani”

Manjo Janar Sami a tattaunawarsa da Manuniya a gidansa dake Kaduna, ya ce sha’anin Boko Haram abu ne da za a iya shawo kansa a cikin kankanin lokaci to amma dayake batagarin yan siyasa sun shiga ciki

“abun ya zama akwai munafunci shi yasa ya gagara a dakile shi” ya ce a zamaninsu sunyi aiki da zuciya daya, kishin kasar ne a zukatan su shi yasa suka samu nasarar tabbatar da Nigeria kasa daya dunkulalliya “amma yanzu abun ya sha bambam”

Sami wanda aka yaye su a soja a 1963 tare da su Muhammadu Buhari wanda kuma ya rike Gwamna a jihohin Benue, Sokoto da Bauchi a zamanin mulkin soja ya ce Shugaba Muhammadu Buhari yana bakin kokarinsa a kasarnan kuma yafi kowane shugaban kasa kawo cigaba a kasarnan musamman ta fannin samar da ababen more rayuwa.

“Mun ga abubuwa daban daban, kama daga lokacinda akayi juyin mulki a 1966, da lokacinda aka kashe su Murtala, ni na hana su Dimka yin juyin mulki a lokacin bayan sun kashe Murtala nan nasa aka kawo mini gawarsa, sannan nasa aka kaishi dakin ajiye gawa har zuwa lokacinda iyalinsa ta zo”

Manuniya ta ruwaito da yake magana game da mulkin Zuru, basaraken yace baya cin hanci da rashawa ko danne wa talakawa hakkinsu saboda Allah ya azurtashi da dukiya,

“Tun da nayi ritaya a 1990 na fada kasuwanci kuma Allah ya sanya wa kasuwancin Albarka, yanzu haka na samarwa mutane da dama ayyukanyi a Zuru, mun kawo cigaba a fannin ilimi da tsaro, a kalla kowace rana nakan kashe dubban kudade tun hawa na mulki yau kusan shekara 26.” Haka muke ta hidima da jama’a da bukatunsu “kuma mun godewa Allah da ya rufa mana asiri”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *