Masu garkuwa sun shiga gidan mutuwa sun yi awon gaba da duka masu zaman makoki a Katsina
Rahotanni da dumi-duminsu daga jihar Katsina suna bayyana cewa a daren jiya Talata yan bindiga sun shiga cikin wani gidan makoki a garin Kofa dake cikin karamar hukumar Kusada sun yi awon gaba da mutane dake zaman ta’aziyya.
Daga cikin mazauna yankin ya bada labari inda Isah Ibrahim ya rubuta karin bayani a shafinsa na Facebook cewa:-
“Innalillahi wa’innah ilaihir raji’un
Cikin dare’ n nan masu garkuwa da jama’a sun shiga cikin garin Kofa dake karamar hukumar Kusada, jihar katsina, inda suka rufta gidan makoki suka tarkata masu zaman makokin suka korasu daji.