Kungiyar UNICEF tana amfani da mata wajen wayar dakan iyaye mata a Maiduguri
Daga Zubairu Lawal
Kungiyar kula da yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta dukufa wajen wayar dakan iyaye mata dasu rika janyo yaransu a jikawajen tarbiyansu.
Misis Mercy Shooto Jayeola itace Shugaban sashin wayar dakan dake na shiyar Arewa maso gabashin Nijeriya a kungiyar UNICEF.
Tace; ba zai yuhu a samu zaman lafiya a wannan shiyar yadda ake bukata ba saboda an saqa gaba baya na warwarewa ne.
Sakamakon ana kara diban yara kanana ana amfani dasu wajen ayyukan Ta’addanci. Tace; Kungiyar UNICEF ta gano hakane ta hanyar ganin suwaye ke kai hare hare a kauyuka? Akasarinsu yarane kanana.
Meyasa ake amfani da yara kanana wajen kai hare-haren Ta’addanci. UNICEF ta gano cewa yawancin yara sunabin shawarar abokansu ba tare da sunyi tunani mai kyau ba.
Kuma iyaye basu janyo ya’yansu a jika suna basu shawarwari da zai amfaneau, bilhasalima wata uwar tana fin shekara ba tare da tayi ido biyu da danta ba iyaka abin da ya turo mata tayi farin ciki.
Hakan ya sanya kungiyar UNICEF ta dibe mata ta koyar dasu dabaru na wayar da kai ta yadda zasu rika shiga gida gida suna wayar dakan iyaye yara.
Matan suna shiga gidaje suna nunatar da iyaye cewa su rika janyo yaransu suna basu kyakyawar kulawa da tarbiya abinda suka samu zasuci su tabbatar sun baiwa yaransu suma suncin wannan su rika nunatar dasu hanyoyi na tausayi da jinkai, su guji mu’amalam da yan Ta’adda da suka sukurkuce masu zaman lafiya yankinsu.
Su koyar dasu hakuri da rashi su jajirce wajen niman ilumi saboda zai amfanesu nan gaba.
Misis Mercy Shooto Jayeo tace a yanzu muna ganin natijar yin hakan saboda da daman iyaye suna tabbatar da jin dadin wannan shawarar.
Daga karshe tace; wannan shirin am fadadashine domin yin amfani a jihar Borno da Adamawa da kuma Yobe.