Zan tabbatar da kabilar Eggon sun koma matsuguninsu dake Assakio inji Gwamna Sule
Daga Zubairu Lawal
Gwamana Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule yace; nan bada jumawa ba alumman kabilar Eggon mazauna garin Assakio dake gudun hijira a wasu guraren zasu koma mazauninsu dake assakio. Hakama yan kabilar Bassa dake zaune a wasu garuruwan zasu dawo matsuguninsu na asali.
Gwamna Abdullahi Sule yace; ba zai yuhu wani yace babu wasu kabilar da zasu zauna a garuruwan da suka fi yawa ba.
Gwamnan yace; gari na kowane kuma Gwamnati bukatarta a zauna lafiya koda an samu sabani tsakani dukkansu yan uwan junane. Duk inda dan jihar Nasarawa yake a cikin jihar to dan gidane. shiyasa bamu da buri face mu tabbatar da zaman lafiyan alummanmu na jihar Nasarawa mu zama tsintsiya madaurinki daya.
Gwamnatinmu ta zone da hadin kai da kaunar jna, babu mai kawo mana bambamci da rarraba
Gwamna Sule ya bayyana hakane ranar alhamis lokacin da dubban yan kabilar Eggon sukayi gangamin nuna goyon bayansu da niman Tazarc 2023.
Tawagar Eggon karkashin jagorancin Hon. Dr. Joseph Haruna Kigbu( Likitan Talakawa) sun tabbatar da goyon bayansu ga Gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule.
Gwamnan yayi kira gay an siyasa dasuyi koyi da halaiyan kirki irin na Dr.kigbu yadda yake taimakawa alumman jihar shiyasa haryanzu yake da farin jininsa cikin alumma.
Haka zalika Gwamnan yayi kira ga masuyin siyasan kabilanci das u sani lokaci ya wuce, yanzu lokacine na mai kayima alumma ba kazoo kace azabe kabilarka ba.
Shima a nasa jawabin Dr. Joseph Haruna Kigbu yayi alkawarin tattaro kuriun alumman kabilar eggon da sauran kabilun dake yankin Lafia dama wasu yankunan domin samun nasarar Gwamna Abdullahi Sule a 2023.