Gwamnatin Nasarawa ta sallame Alhazai sama da 600 zuwa kasar Saudiyya
Daga Zubairu Lawal
Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule yayi ban kwana da Alhazan Jihar Nasarawa kimanin 684 da zasu samu damar sauke farali a kasa mai tsari.
Gwamna Abdullah Sule yace; Hajji kirane na Ubangiji duk wanda yasamu damar zuwa sauke farali ya nutsu ya gudanar da aikin tsakaninsa da Allah.
Gwamna Abdullah Sule yace; bana Allah yasa za a samu gudanar da aikin Hajji sabanin shekaru biyu da suka shude saboda annobar cutar Covid-19.
Gwamnan yace; wadanda suka samu wannan damar su taimakawa Nijeriya da adu’a Allah ya kawo zaman lafiya mai daurewa.
Haka zaliqa ya ummurci Alhazan dasu zamo jakadu na gari, domin gyara sunan Nijeriya a idon duniya.
Gwamnan ya nada Shugaban Majalisan dokokin jihar Alhaji Balarabe Abdullah a matsayin Amirul-Hajji na bana da zai jagoranci mahajatar.