Nasarar Hajara Dan Yaro zai karawa Mata kwarin giwa a siyasan Nasarawa

Nasarar Hajara Dan Yaro zai karawa Mata kwarin giwa a siyasan Nasarawa

Daga Zubairu M.Lawal

A ranar Juma’a 3/6/2022 aka maimaita zaben fidda gwani na yan takarar kujerar Majalisar dokokin jihar Nasarawa, karkashin Jam’iyyar APC.

An dai maimaita zaben a mazabar Nasarawa ta tsakiya dake cikin karamar hukumar Nasarawa.

Zaben ya gudana a masaukin baki na tsangayar kimiya da fasaha dake garin Nasarawa.

An gudanar da zaben ne cikin tsaro karkashin jagorancin kwamitin zabe mai mombobi 7 Wanda Sadeeq Shehu ya jagoranta a matsayin malamin zabe.

Zaben da gudumomi 7 suka gudanar domin samun wakilcin wanda zai tsaya takara domin fuskantar babban zabe a APC

Yan takarar sun hada da Hajara Ibrahim Dan Yaro da Hon. Sulaiman Dan Baba wanda yake kan kujerar.

Beyan tantance masu kada kuri’an da yawansu ya kai 35 inda kowannensu rike yake da shedar katin da ake bukata da kuma sunansu cikin littafin.

Bayan kammala zaben an kidaya kuri’an inda Hajiya Hajara Ibrahim Dan Yaro ta lashe zaben da kuri’a 35.
Duk da cewa abokin karawar nata bai zo filin zaben ba, kuma bai turo wakili ba. Amma Malamin zaben Sadeeq Shehu ya tabbatar da sahihancin zaben.

Yace; sauran yan takarar basu zo ba kuma basu turo wakilai ba duk da cewa sunsan da maimaita zaben a wannan ranar.

Malamin zaben ya sanya hannu yare da dukkan wakilan zaben inda aka mikawa Hajiya Hajara Ibrahim Dan yaro takardan shedar lashe zaben.

Hajara Ibrahim Dan yaro, tayi godiya ga Allah da ya nuna mata wannan ranar na samun muhimmin nasara. Ta kuma godewa al’umman Nasarawa da suka fito suka nuna mata kauna suka jajirce da nuna soyayyanta.

Hajiya Amina wata yar siyasace a garin Nasarawa tace nasarar Hajara zai karawa mata kwarin giwa a siyasan jihar Nasarawa.

Saboda mata suna fitowa takara amma da dama basu wauce matsyin fidda gwani ake kadasu. Yanzu jajircewa da Hajiya Hajara Ibrahim Dan yaro tayi abin alfaharine ga sauran mata.

Tace yanzu mata zasu samu kwaringiwa su fito su zuba kuri’a so sai. Domin mata suke da kuri’a a hannu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *