YA TABBATA JIKA YA FICE DAGA JAM’IYYAR APC?*

  1. *YA TABBATA JIKA YA FICE DAGA JAM’IYYAR APC?*

Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta Tsakiya a jam’iyyar Apc Hon.Halliru Dauda Jika ya tabbatar da ficewarsa daga tsohuwar jam’iyyarsa ta Apc.
Ya bayyana haka ne a cikin wasikar da ya rubuta wa shugaban jam’iyyar na gundumar da ya fito, Gundumar Kafin madaki da ke karamar Hukumar Ganjuwa jihar Bauchi.

Sanata Jika wanda shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin ‘yan sandan a Majalisar Dattawa.
Duk da cewa cikin takardar da ya rubuta wa tsohuwar jam’iyyar tasa bai bayyana jam’iyyar da ya komaba amma tuni yaransa da abokansa na siyasa suka cika Shafukan sada zumunta da Hotunansa wanda suke nuni da komawarsa Jam’iyyar NNPP mai kwadon kayan marmari kuma a nan ake kyautata zaton zai yi takarar kujerar Gwamnar Jihar Bauchi.
Munyi kokarin ji daga gareshi amma abin yaci tura sakamakon rashin samunsa a waya amma duk da haka mun tura masa sakon Kar ta kwana da zaran munji daga gareshi za kuji karin bayani.

~Alh.lawal k.madaki
19/6/2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *