An yabawa Dr. Ikrama Hassan Shugaban Asibitin Dalhatu Arab dake Lafia
Daga Zubairu M Lawal
Jama’a da dama sun yabawa Shugaban Asibitin Dalhatu Arab dake garin lafia fadar Gwamnatin jihar Nasarawa.
Bayan Gwamnatin jihar ta kara musanya masa kwantiraginga na cigaba da jagorantar tawagar ma’aikatan Asibitin Dr. Ikrama Hassan ya samu yabo wajen al’umman jihar Nasarawa.
Gwanna Abdullah Sule na jihar Nasarawa ya duba chancanta da yadda Dr. Ikrama Hassan ya kawo cigaba da sauye sauye na tsarin hana cinkoso cikin Asibitin da yadda yake kula da kaddarorin Gwamnati a cikin Asibitin ya sanya Gwamnatin taga chancantar ta kara masa kwantiragin cigaba da jagorantar tafiyar da Asibitin.
Kungiyoyin Likitoci dabam dabam da sauran Ma’aikata sun bayyana farin cikinsu a fili da jin dadinsu saboda yadda aka dawo da Dr. Ikrama Hassan.
Dr. Ishaq Muhammad Ma’aikacine a cikin Asibitin yace: zuwan Dr. Ikrama Hassan gaskiya an samu cigaba sosai saboda ya samar da sauye sauye masu amfani.
Yace; Dr. Ikrama yayi tsayin daka wajen baiwa Gwamnati shawara ta samar da Na’urorin zamani na binciken manyan cututtuka.
Yace; yanzu haka a cikin Asibitin nan akwai Na’urar binciken cututtuka da ba kowani Babban Asibitine zaka sameshi ba.
Yace; Dr. Ikrama ya sanya ido wajen kulawa da wadanan Na’urorin.
Shima Dr. Sabo Samuel ma’aikacine a fannin tiyata cikin Asibitin Dalhatu Arab.
Yace; a baya ana samun matsaloli masu yawa a cikin Asibitin nan. Saboda ko ta fannin ajiyar ababen hawa. Da zarar ka ajeye abin hawanka ka shiga bakin aiki hankalinka na waje wajen abin hawanka saboda yadda sace sace yayi yawa.
Amma zuwan Dr. Ikrama Hassan ya dauki mataki wajen sanya jami’an tsaro masu zurga zurga da bincike cikin Asibitin.
Yace; yanzu koda abin hawanka zai kwana a cikin Asibitin baka da fargaba.
Ya kuma yabawa Dr. Hassan Ikrama kan yadda yake kulawa da Ma’aikata da kuma basu shawarwari mai amfani.
Itama Hajiya Husaina Ibrahim mai’aijaciyace a Asibitin Dalhatu Arab ta yabawa Dr. Ikrama Hassan kan yadda ya ke gudanar da aiki tsakani da Allah.
Tace; yana kulawa so sai kuma kowa ya shigo cikin Asibitin Dalhatu Arab yasan an samu sauyi mai yawa.
Ta kuma Shawarci Dr.Ikrama Hassan kan yadda Asibitin keda Na’urorin zamani na kiwon lafiya ya kamata a kara yawan kwararun likitoci, saboda wadanda suke nan sunyi kadan aiki yana masu yawa.
Tace; duk fadin gari Lafia babu Asibiti kamar wannan kuma jama’a suna yawa a kullun kuma har yanzu Asibitin bata da wadatattun likitocin da ake bukata.
Tace; yawan jama’an dake zuwa Asibitin sunyiwa likitocin dake dubasu yawa.
Tace; akwai kyakyawar fahintar juna yanzu tsakanin kungiyoyin Ma’aikata Asibitin da Shugaban Asibitin Dr. Ikrama Hassan.
Tace; ko abaya rashin fahinta ne da kuma masu bakinciki da sabin tsarin da Dr.Ikrama ya shigo dasu. Amma yanzu kowa yaga amfanin hakan da cigaban da aka samu.
Shuma majinyata dake kwance a Asibitin suna bada labarin yadda suke samun kulawa daga Ma’aikata jinya na Asibitin.
Ta yadda Ma’aikata ke gudanar da ayyukansu akan lokaci dare da rana.
Sannan ana kuma tsaftace Asibitin gwanin ban sha’awa.