KO KUNSAN : Talakawa na fuskantar zama cikin duhu a jihar Nasarawa ?
Daga Zubairu Lawal
Al’umman jihar Nasarawa sun fara yanke tsammani da samun wutan lantarki a gidajensu da shaguna saboda tsadar.
Bayan gyara wutan lantarki da Gwamnatin jihar tayi inda yanzu wutan lantarki ke dan samu a wasu sassan jihar Nasarawa.
Tunidai al’umman jihar sun fara tunanin yin ban kwana da wutan lantarki a fadin jihar.
Kudin wutan lantarki mafi sauki da kamfanin raba wutan lantarki mai suna (Abuja Electricity Distribution Company) AEDC ke mikawa a gidajen Talakawa daga N15,000 zuwa sama.
Lamarin da ya tsorata mutani ganin yadda rayuwa tayi tsada ana hannu baka hannu kwarya.
Mutani da dama masamman masu kananan karfi sunfi kokawa, saboda wani gidan babu komai sai kwai dake haska gidan amma ana kawo masa N15,000?.
Hakan ya sanya da daman mutani sun amince ma’aukantan Wutan lantarki da sunzo suyanke wutan su mika masu wayansu.
Da dama gidaje suna kokawa kuma sukan yarda a yanke wutan a barsu da wayoyinsu. Da biyan zunzurutun kudaden gara zama cikin duhu.
Da dama sun shedama wakilinmu cewa a watan da ya gabata an kara masu kudin wutan lantarki daga N3000 zuwa N5000, Amma a wannan watan an kawo 15,000 zuwa 20,000.
Har ya zuwa yanzu Gwamnatin jihar Nasarawa batayi wani gansashen beyani kan wannan tsadar wutan lantarki ba.