KU KARANTA – Farashin Man Fetur Gwamnatin Tarayya ta bambamta matsayin Arewa da kudu

KU KARANTA – Farashin Man Fetur Gwamnatin Tarayya ta bambamta matsayin Arewa da kudu

A ranar Talata, Yuli 19, 2022 Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya rattaba hannu kan saida Kamfanin Mai ta Kasa NNPC sannan Gwamnatin ta bayyana tsarin jaddawalin yadda kowani yanki zai sai da man Feturu a kasar.

Masu amfani da man fetur a Najeriya za su ga canji yayin da suka shiga gidajen mai daga ranar Babu wanda zai sake saida man fetur a kan N165, Gwamnati ta amince da karin N4 zuwa N24.

Gwamnatin tarayya ta amince da karin farashin litar fetur daga N165 da aka sani a gidajen mai zuwa akalla N179, da da N184 da N189.

karin da kamfanin NNPC suka yi ya fara aiki daga rabar Talata, 19 ga watan Yuli 2022 a gidajen man kasar nan.

NNPC ta sanar da ‘yan kasuwa cewa su canza farashin da suke saidawa mutane litar man fetur.

Farashi a kowane yanki Kamar yadda mu ka samu labari, wannan karo sauyin farashin ya danganta ne da yanki, maimakon duk kasar.

A yankin Kudu maso yamma, daga N165, za a koma saida lita a kan N179, an samu karin N14. A Arewa maso yamma daga N165 zuwa N184 an yi karin N19 kenan.

Arewa maso gabas za su ga karin har N24 a duk lita daga N165 zuwa N189.

‘Yan Kudu maso kudu za su koma sayen fetur a N179. Karin N19.

A Legas ne inda aka inda Gwamnatin tayi masu gata zasu saya Fetur kan N169 karin N4 kachal.

Ita kuwa birnin tarayya Abuja karin N9 ne zasu saya kan N174.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *