Sadio Mane ne gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2022
Sabon dan wasan Bayern Munich Sadio Mane ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2022.
Karo na biyu kenan da dan kwallon tawagar Senegal ya lashe kyautar, bayan da ya dauka a 2019 daga nan ba a gudanar da bikin ba, saboda cutar korona.
Tsohon dan wasan Liverpool ya yi takara tare da Edouard Mendy dan wasan Senegal da Chelsea da kuma Mohamed Salah na Masar da Liverpool.