” Ko kuyi biyayya ga APC ko ku ajiye mukamanku Ku fice daga jam’iyyar ” – Gwamnan Nasarawa

” Ko kuyi biyayya ga APC ko ku ajiye mukamanku Ku fice daga jam’iyyar ” – Gwamnan Nasarawa

Daga Zubairu Lawal

Gwamna Abdullah Sule na jihar Nasarawa ya gargadi   masu rike da mukaman siyasa da su cigaba da biyayya ga APC ko kuma su fice daga Jam’iyyar.

Gabanin zaben 2023, Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya gargadi masu rike da mukaman siyasa sama da 200 da su kasance masu biyayya ga Gwamnatinsa, da kuma jam’iyyar APC ko kuma su yi murabus.

Gwamna Sule ya yi wannan gargadin ne a wata ganawa da ya yi da daukacin masu rike da mukaman siyasa, a gidan Gwamnati a ranar Litinin.

A cewar Gwamnan, duk da cewa ba shi da niyyar korar kowa, amma ya yi kira ga wadanda abin ya shafa da su sauya salon tafiyarsu su kasance masu biyayya ga Gwamnatinsa ko kuma su yi murabus daga mukaminsu.

“Ba na son korar kowa, na yi imanin cewa yana da kyau a fara tambayar mutane cikin mutunci, ko dai su canza salon biyayya ga Gwamnati ko kuma su fice daga cikin Gwamnati.

Gwamnan ya bayyana cewa, a fili, wasu daga cikin masu rikeda mukaman siyasa ba sa daukar kansu a matsayin wani bangare na Gwamnati, suna baiwa wasu hadin kai a waje.

“Abin da mai hankali da mutunci ya kamata yayi. Idan har zai yi biyayya ga wasu dabam ya kamata ya ajiye mukamin Gwamnati dake hannusa, ko ya fice daga jam’iyyar APC”.

Akan shawarar mayar da mulki zuwa Kudu, ya bayyana cewa, wasu Gwamnonin Arewa sun tashi tsaye wajen nuna adawarsu da wannan tsarin.

Ya kamata jagororin Jam’iyya su zage dantse wajen janyo hankalin mombobin Jam’iyyar APC domin hada kai a fuskanci Babban zaven 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *