Rikicin APC zamu dauki mataki bisa tsarin doka kan Shugaban Matasan APC a Nasarawa – Shugaban Jam’iyya na Ciroma

Kwamiti ta mika Rohotu kan binciken Shugaban mtasan APC a Nasarawa

Daga Zubairu Lawal

A ranar Asabar 29/10/2022 kwamitin Alhaji Labaran Maina ta mika rohotun da tayi bincike kan Shugaban matasa na jam’iyyar APC a jihar Nasarawa.

Kwamitin Wanda Shugabannin Jam’iyyar APC ta gudumar Ciroma dake Karamar Hukumar Lafia, nane gudumar da Shugaban matasan Honorabul Abdullahi Masi ya fito, ta kafa karkashin jagoranci Alhaji Labaran Maina da mutani hudu.

Kwamitin binciken ta mika bayanan ta kundin takardu guda uku.

Da yake bayani Shugaban Kwamitin Alhaji Labaran Maina yace; wannan kwamitin tayi aikine tsakaninta da Allah ba tare da son zuciyar wasu ba.

Yace; sun gudanar da aikinsu yadda sukabi didigin abin da yafaru ba tare da nuna shakku ko tsoro ba.

Kuma sun gudanar da komai da ya dace su gudanar na tsawon kwanaki sha hudu yanzu sun mika sakamakon binciken ga wadanda suka nadasu.

Shima a nasa jawabin Shugaban gudumar Ciroma dakeLafia cikin jihar Nasarawa Hon. Muhammad Sulaiman yace; munyi jimami da wannan matsalar da ya samu da Dan uwanmu Shugaban matasa na Jam’iyyar APC ta jihar Nasarawa. Kuma take mukabi tsarin da Jam’iyyar APC ta tanada kan duk Wanda aka samu da wannan matsalar na a dakatar da shi sannan ayi bincike.

Yace; yanzu kwamitin ta gabatar da rohotun bincike zasu duba su gani sannan su mikata zuwa karamar hukuma.

Hon. Muhammad Sulaiman ya qara da crwa komai yanada dokakinsa daki daki sai anbi daki sai a samu zaman lafiya.

Zasu duba su gani duk abinda doka tace shine zasu dauka saboda kiyaye gaba.

Tun a ranar 9/10/2022 ne aka dakatar da shugaban matasa na Jam’iyyar APC ta jihar Nasarawa sakamakon furta wasu kalamai na rashin da’a ga jagororin Jam’iyyar ta jihar.

Kalaman da wasu ke dangantawa da cewa cin fuskane ga Gwamnan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *