Kwanaki uku kafin tawagar Faransa ta fara buga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2 a Qatar, dan wasan kasar da ya lashe kyautar Ballon d’Or, Karim Benzema, ya fice daga gasar saboda rauni da ya samu a cinyarsa.Labarin cewa Benzema ba zai buga gasar cin kofin duniya karo na uku a jere ba, ya jefa kasar da ke rike da kambun gasar cikin wani yanayi.
Faransa dai ba za ta buga wasanta da N’Golo Kante da Paul Pogba ba, sakamakon rauni da suka samu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Benzema ya ketare gasar cin kofin duniya ta FIFA ba, domin ko a shekarar 2010 da 2018, dan wasan ya gaza samun damar fafatawa a gasar ta cin kofin duniya da aka yi a kasashen Afirka ta kudu da Rasha.
Ko me ya hana shi buga gasar cin kofin duniya ta 2010?
Lokacin da kocin Faransa Raymond Domenech ya yi watsi da Benzema a shekara ta 2010, hakan ya faru ne bisa zarginsa da rashin daidaito da Real Madrid, inda a yanzu ya haskaka a matsayin babban tauraro da ke bawa kungiyar ta Spain gudun mowa sosai.
Zargin cin zarafi da ya shafi Benzema na daga cikin dalilin da ya sa ba a zabe shi ba, amma sauran ‘yan wasan da su ma aka zarge su tare da shi a wancan lokacin sun shiga jerin sunayen tawagar Faransa a gasar.
A zahiri Benzema zai ci gaba da buga gasar cin kofin duniya ta FIFA a Brazil a shekarar 2014, amma makamantar zarge-zargen da ake masa sun hana shi halartar gasar.
Dalilin da ya hana Benzema halartar gasar a 2018
Ba a sanya sunan Benzema a tawagar da ta wakilci kasar a shekarar 2018 da aka fafata a kasar Rasha ba, kuma kocin Faransa Didier Deschamps bai bayyana dalilan da suka haddasa hakan ba a wancan lokacin.
Benzema, duk da haka, ya sake fuskantar wani zargin na batanci ga abokin wasansa, Mathieu Valbuena da ke takawa Faransa leda.
An tuhumi gwarzon dan wasan na duniya da masaniya kan faifan bidiyon ya yi yamadidi a kafafen sada zumunta wanda ke dauke da tsiraicin dan wasan.
Hukuncin da kotu ta yanke a wancan lokacin shine, sai an dauki tsawon shekaru biyar kafin a kira Benzema zuwa tawagar kasar Faransa, to said ai kuma daga bisani dan wasan ya lashe kyautar Ballon d’Or.
Yana shirin zama daya daga cikin shidan farko da za su haska gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar, amma raunin da ya ji ya bar Faransa da raunin fatan taka rawar gani a gasar, kasancewar ta matsayin zakara